Yadda 'Yan Mata Suke Zubar Da Damar Su A Shekarun kuruciar Su - Android Pols
Ita Mace, idan tana shekaru 16-21, kamar kwallon kafa take kan farin jini, Mutum 22 a fili, kowa na so ya nuna bajintarsa don ya sami nasara. Ita kadai, suna ta rubibinta.


Idan mace takai shekara 22-25 sai ta koma kamar Kallon kwando. Mutum goma ne ke gasar nuna bajinta akanta. Mai rabo ya samu.


Daga shekaru 26-30, sai ta koma kamar kwallon tebur. Mutum biyu ne ke fafatawa tsakaninsu wanda yayi nasara ba wata murnar kirki yake ba.


Idan shekarunta sun kai 31-35 kuwa, kamar kwallon Gora (golf) take komawa. Mutum ya buga a barsa, idan ta fada rami ya dauko idan ma ta wuce ya dauko. Shi yake fama shi ka dai ana kallonsa.


A nan, ne in abubuwa ba su tafi yadda ake so ba, sai ta koma yar kungiyar kare hakkin mata da yara. 


A shiga rediyo ana zagin mazaje ana hure kunnen matan da Allah ya sa hakonsu ya cimma ruwa suke tsugune gidan mazajensu.


Da fatan 'yan mata za'a koyi darasi daga wannan rubutu kuma da da fatan za ku gyara halayen ku. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post