Takaitaccen Tarihin Abdurahaman Bin Auf R.A - Android PolsSunansa

Abdurrahaman Dan aufi Dan Abdulharis, mahaifiyarsa sunanta Shaffa'u diyar Aufi, ta musulunta kuma tayi hijira.


A lokacin jahiliya ana kiransa da Abdu Umar, ko kuma akace Abdulharis, Annabi SAW ya ambaceshi da suna Abdurrahaman sadda ya musulunta.


Anhife shi bayan shekarar giwaye da shekara goma 10, tun yana kuriciyarsa yakasance yana nisantar bautar Gumaka baya shan Giya.

Ya kasance attijirine yana zuwa Yamen Dan kasuwanci, ga Amana da cika alqawari da gaskiya a kasuwancinsa.


Abdurrahaman yana daya daga cikin Asharatu bil Janna, yana cikin Ashabu Shura 6, sannan anyi hijira biyu dashi zuwa habasha, yayi hijira zuwa madina, ya halarci dukkan yakoka tare da Annabi SAW kuma yatabbata tare dashi a ranar yakin Uhudu, a wannan yakin Uhudu yasamu rauni na suka har 20.


Sayyidi Abdurrahaman RA yakasance mai yawan ciyarwa da sadaqa sannan  yabada dukiyarsa acikin daukaka kalmar Allah da iyanta bayi, an ruwaito cewar ya iyanta bayi 30,000.


Shine wanda Annabi SAW yayi Sallah a bayansa


Sayyidina Abdurrahaman yasamu wani matsayi mai girma wanda ANNABI SAW yayi Sallah a bayansa, Annabi SAW baiyi sallah a bayan wani mutum daga cikin al-ummarsa ba face bayan sayyidina Abubakar Siddiq da kuma Abdulrrahaman Dan Aufi.


Siffarsa.


Mutunne mai tsawo, sannan farine wanda aka cudanyashi da Ja, mai kyakkyawan fuska, mai yalwar idanuwa, mai manyan tafuka, mai siririn gashi, mai madaukakin hanci mai kaurin 'yan yatsu.


Wafatinsa


Yayi wafati Hijira na da shekara 32, yayi wafati yana da shekara 75 an birneshi a Baki'a RA, Sayyidina Usman yayi masa sallah kamar yadda yayi wasiya.

Allah yakara jadda kusancinsa da Manzon Allah SAW.

Wallahu A'alamu


Allah yakara mana taslimi da soyayya ga Annabi SAW da sahabbansa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post