Siffofi Goma Sha Ɗaya Da Mace Ta Ke So Daga Namiji - Android Pols
Akwai wasu halaye na maza da duk Mace Ke burin ta samu. Sai dai ba duka maza ne suke da irin wannan halayen da mata suke so ba. 


Ga jerin wasu daga cikin halayen maza da mata ke burin aura kamar haka:


1. Namiji mai tausayi

Mace tana son namiji mai tausayi ba mai kaushin zuciya ba da saurin duka. Tana son mutum ya zamto ko faɗa zai mata ya yi cikin hikima ba cikin fushi da tashin hankali ba.


2. Namiji Mai Girmamawa 

Mace tana son wanda zai girmama ta ba wanda zai tozarta ta da gori ba. Don akwai mazan da basa girmama matansu ko kadan 


3. Namiji Mai Kuzari 

Duk Mace tana son samun namiji ƙaƙƙarfa mai lafiyar da zai iya biya mata buƙatar ta aure ba ragon namiji da ba ya iya yin wani abin kirki ba.


4. Namijin Da Bai Da Girman Kai 

Mace tana son namijin da yake amsa kuskurensa idan ya aikata. Mata Suna son idan an yi musu Kuskure a nemi yafiyar su, wanda ba kowane namiji ne yake iya baiwa mace hakuri ba duk irin laifin da yai mata. 


5. Namiji Mai Kyauta. 

Mace tana son namiji mai karamci, alheri ba ƙanƙamo ba.


6. Mace tana son namijin da ya yarda da kansa.


7. Ba ta son namiji mai nauyin jiki da kasala wanda zai ta wahalar da ita.


8. Mace tana son namijin da zai sa ta farin ciki ta ji cewar ta cika mace. Ba wanda in ya doso gida za ta dinga fargaba ba, ba za ta sake walwala ba sai ya fita.


9. Tana son namijin da ke son ta don Allah ba don dukiya, matsayi ko kyanta ba. Domin ta san idan waɗannan abubuwa suka ƙare watsar da ita zai yi.


10. Mace tana son namiji mai wayo kuma mai haƙuri.


11. Tana son namiji mai dogon tunani kafin ya yanke hukunci. Wanda ko rai ta ɓata masa ba zai yanke hukunci ba sai ya yi tunani.


da fatan maza za su ɗauki darasi.


Ubangijina Allah ya sa mu dace da irin matan/mazan da muke kauna da muradi a Rayuwar mu ta aure. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post