Shekaru 50 Da Fara Hidimar Kasa Ta NYSC Tun Daga 1973 - 2023, Android Pols



A Rana mai Kamar Ta Yau 22 Ga Watan Mayu 1973 A Lokacin Zamanin Mulkin Soja Na Janar Yakubu Gawon Aka Kirkiro Da Hukumar Yiwa Kasa Hidima Ta NYSC. 


Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) wani shiri ne da gwamnatin Najeriya ta kafa a lokacin mulkin soja domin shigar da daliban Najeriya da suka kammala karatu a fannin gina kasa da kuma ci gaban kasar. tun a shekarar 1973 aka bukaci daliban da suka kammala karatu a jami'o'i da kuma kwalejin kimiyya da fasaha ta kasa su shiga shirin bautar kasa na tsawon shekara daya.  Wannan ana kiranta da shekarar hidimar ƙasa. Ahmadu Ali ya yi aiki a matsayin Darakta-Janar na NYSC na farko har zuwa 1975. Babban Darakta mai ci Yusha'u Dogara Ahmed.


An kirkiro NYSC a ranar 22 ga Mayu 1973 a matsayin hanyar sulhu, da sake gina kasa bayan yakin basasar Najeriya Da Akayi A Tsakanin Shekarun 1967 Zuwa 1970. An kafa ta ne bisa doka mai lamba 24 wadda ta bayyana cewa an kirkiro shirin ne "da nufin karfafawa da bunkasa alaka tsakanin matasan Najeriya da kuma inganta hadin kan kasa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post