Samun Ni’ima A Saukake, Saka Mai Gida Kukan Dadi - Android Pols
Albisbirin ki yar’uwa, Shin kin san za ki iya samun ni’ima a saukake? ki hada magungunanki na mata da kanki? ba sai kin kashe makudan kudade (dubunnai) wajen siye ba, Naira 500 ko 1000 ya ishe ki. Kuma ma, za ki fi jin dadin amfani da shi saboda ke kika hada kayanki, ba a waje ki ka saya ba balle ki yi ta fargaban da me aka hada.


Wallahi-wallahi akwai masu maganin da basa gyara ko tsince datti zasu bayar a niko musu kaya kuma su siyar wa bayin Allah. Akwai kuma wanda suke mix, su hada da wasu kayyaki na daban don yai musu auki su samu riba.


Ga Kadan Daga Abubuwan Da Za kiyi Don Samun Ni’ma A Saukake, Tsarki da ruwan zafi (dumi) ko kuma ki tafasa bagaruwa ko ganyen magarya kina tsarki da ita.


Ki jika Lipton idan ya jiqu saiki fasa danyen kwai aciki ki kada sosai sannan ki shanye.


ki samu kanumfari ki zuba ruwa ki tafasa ki tace, sai ki zuba madararki na ruwa ko gari ki sha. madara kisha.


Ki samu kankanarki ki nika ta a blender ki zuba madara da zuma ki shanye. Idan ba’a samu blender ba za ki iya yankata kanana.


Za ku iya shan wannan hadin tare da mai gida don a ji dadin harka tare don ruwan kankanar ya ratsa jikin kowannen ku. Wallahi bayan kin sha wannan hadin da kanki za ki ji canji a jikinki.


Ki samu garwashin wuta ki zuba turaren wuta ko kanumfari kadan kidan tsuguna akai. idan yashiga jikinki haka zaki ringa kamshi ga kuma matsi da ni’ima.


ki samu lalle 1cup ki zuba ruwa dai-dai misali idan ya ta fasa ki juye a roba mai fadi, sai ki bari ya huce kadan sannan ki shiga ciki ki zauna kamar na minti talatin. hakan zaisa ki matse ga kuma karin Ni’ima. ki samu zuma mai kyau ki ringa shan cokali uku safe da yamma. ki samu garin hulba ki dama da madara ko madarar shanu ko kuma nono ki ringa sha.


ki sami man zaitun ki soya kwai dashi ki ci da safe kafin ki ci komai, kisami budurwar kaza wadda bata fara kwai ba. ki yanka wuyan kawai amma banda cikin sai ki fige abarki, ki zazzage kayan cikin ta ga ba ki daya, sai ki dora ta a wuta, ki zuba nonon rukumi (shi zai dafa ta a matsayin ruwa) sai kuma ki zuba mata garin ridi da duk kayan hadin ki ki san ana farfesu dashi. albasa, attarugu, maggi, gishiri da sauransu. kidafa ki cinye tsokar banda kashi ki shanye romon.


 (Wannan hadin yana zama a jikin mace na tsawon wata 6 ko da ba ta sha komai ba. wasu ma sun ce har sai ta haihu tukuna ta sake yin wani.


ki samu aya, gyada, alkama, waken suya, ki dan soya su sosai sai ki nika su ki ringa damawa kamar kunu kina sa madara kinasha, yana mutukar gyara nono, gyara jiki da karin ni’ima. Masu jego ko wadanda suke shirin yin yaye za su iya sha akai-akai don karin ruwan nono da kuma hanashi langwabewa kamar silifas.


ki sami sassaken kuka ki jikashi ki ringa sha kullum a matsayin tsumi. Yana kawo ruwan ni’ima sosai da sosai wlh, tested and trusted.

Ki nika kankana da dabino ki sa madara ki shanye. Yana karo ruwan ni’ima sosai.


Ki yawaita cin kwadon zogale ko miyanshi ko a tafasa ruwan a yawaita sha. Wallahi duk ranar da ki sha ruwan ta sai oga ya ji ki daban.


Ki samu sassaken baure da mazarkwaila ki dafa ki dinga sha. ki samu tafarnuwa ki jajjagata ki goga ruwan a jikin pad ki dan diga man zaitun kadan, yana maganin infection (ciwon sanyi) kuma yana kara ni’ima.


Da fatan mata za su amfana daga wadannan hanyoyin na samun Karin Ni'ima ga jikinsu

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post