Matsalolin Da Samari Da 'Yan Mata Ke Fuskanta Kafin Aure - Android Pols
A yau idan kace zakayi aure, daga ranar da ka fara neman matar auren, zuwa ranar auren ka, idan bakayi sa'a ba sai wando ya daina zama a kugun ka saboda tsadar aure da irin yadda Amarya zata dinga tatsarka Irinsu: kudin nagani inaso, kayan amfanin yau da kullum, kudin saka rana, sadaki, kayan lefe da kudin gaisuwar uwa da uba da sauran su.


Wannan yana daga cikin manyan abubuwan da ya sanya samari da dama suka gaza yin aure a wannan zamanin.


Amma yau idan saurayi yayi niyyar yin zina a rana daya indai yana iyawa zai iyayi da mata 20 ko sama da haka, kuma kudin da zai kashe ba zai kai dubu hamsin ba, wasuma ko sisi basa kashewa, kyauta suke yi.


Saboda yanmatanan gasunan birjik. kamar tuwon gidan biki kuma suna bukatar auren amma samari ba kudi, iyaye kuma kudin suke so.


Wannan yana daga cikin dalilin da yasa aka taru aka hada karfi da karfe tsakanin shaidan, samari da yanmata ake sa6awa Allah kullum.


Zina kuwa na daya daga cikin manyan laifuka masu kawo fitintinu a wannan duniyar tamu.


Hanya ta farko da za'a bi domin kawo karshen zinace-zinace, shine farashin aure ya fado kasa warwas! Bawai kuma darajar auren ba, a'a al'adun dake hana auren, domin babban abun bujata a aure shine sadaki, shima idan babu ana badawa bashi. 


Duk fa musulunci yayi hakane domin a rage fasadi a doron kasa. Amman duk da haka auren bashi ban ta6a jin anyi ba idan ba'a karin magana danake ji suna cewa: "fallasa auren bashi ba".  A daya bangaren kuma zina akan yita a bashi. 


Wani abun takaici ma shine, idan wannan shekaran farashin sadaki na dubu hamsi ne, toh tabbata shekara mai zuwa a dubu tamanin zaka ji shi.


Sai dai inaga farashin sadaki yana yin tsadane bisa dalilin talauci da ake fama dashi, domin ko nawa iyayen yarinya suka amsa a matsayin sadaki basu ke cinyewa a cikin su ba, karawa kudin yawa suke domin su yiwa yar tasu kayan daki dan a fita kunya. Kowa yasan wannan kam, yawancin lokuta. 


Ita kuma kunya anaso a fice tane a gurin 'yan gutsiri tsoma, wadanda idan ba'ayiwa yarinya kayan a-zo-a-gani-ba, za su bi unguwa suna gulmace-gulmace, karshe ya koma gori wajen Amarya. Wannan ke sanyawa wasu iyayen tsauwala kudin sadaki.


Toh amma, sai suka manta cewa ita kunya ta Ubangiji ake gudu, ba ta wani abun halitta ba. 


Domin idan diyarka tayi cikin shege a gidanka sai kafi kowa jin kunya a duniya, kuma wannan shine abin kunya da ake gudu, ba kunyar kayan lefe ko sadaki ba. 


Iyaye su cire kunyar abun halitta suji kunyar Mahalicci, su cire wadannan al'adun dake hanasu aurar da ya'yansu mata. Idan saurayi yazo neman auren yarinya kace dashi baka bukatar komai daga gareshi bayan sadaki,  don haka kaima kada yayi tsammanin wani abu wai da sunan kayan lefe daga gareka. 


Kuma samari kuji tsoron Allah, idan kunada hali zaifi dacewa inaga idan kunsan gidansu wacce zaka aura fama sukeyi, Maimakon kaje kayi wasu saitunan akwatuna da suke kashe kudi a kalla dubu 250 zuwa sama, zaifi dacewa ka dauke musu nauyin gado, kujera, labule, carpet, TV kam daman kana dashi a dakinka, ka taho dashi. Toh Insha idan samari na haka toh fasadi a doron kasa zai ragu sosai. 


Allah muke roko Ya dauramu akan dai-dai ya aurar da marasa auren dake cikinmu wanda ke da auren ya saukar da rahama da nutsuwa a gidajensu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post