Magungunan Mata Da Yadda Ake Hada Su - Android Pols

 


Duk mutumin da yake son ya samu karfin mazakunta to sai ya samu danyar albasa sai ya yayyankata a soya da man zaitun, sai tayi ja sai a fasa danyen kwai a kada shi da garin habba sai a zuba a sama in ya soyu sai a rinka ci kullum da yardar Allah za a dace.


Maganin Aljanu;

wanda yake so Allah ya kareshi daga kamuwa da matsalar jinnu, duk lokacin da ya dawo gida sai yace bismillahi manzon Allah (S.A.W) yace Allah zai hana duk wani aljani shiga wannan gidan, sannan mutum ya rinka cin habbatussauda cikin abinci kuma ya rinka shafa man habba idan zai kwanta bacci.


Ciwon Sanyin Na Mata;

Sai ki sami garin habbah cokali daya(1) garin hulba cokali daya(1) sai a tafasashi, sai a dan diga zaitun kadan, sai a rinka tsarki dashi, bayan ya tsane sai a rinka shafa man habba, sau ukku a rana. 


 Zubar Gashi Na Mata;

sai ki samu sim-sim da jir-jir cokali goma(10) ko sama da haka sai ki hadasu da man habba karamar kwalba sai ki rinka shafawa safe da yamma.


Don Fuska Tayi Kyau;

Sai ki samu zuma mai kyau sosai ki hada da lemun tsami ki rinka shafawa, bayan minti talatin(30) ko sama da haka sai ki wankeshi da ruwan dumi, bayan nan kuma sai ki samu man zaitun mai kyau sosai ki rinka shafawa.


Rashin Rike Fitsari;

Duk mutumin da baya rike fitsari sai ya samu zuma mai kyau ya rinka hadawa da garin hulba ya rinka sha sau ukku a rana(x3)


Cututtukan Mata;

Sai ta samu garin zaitun da garin hulba ta rinka dafawa da zuma ta rinka sha safe da

yamma.


Matsalar Nakuda Da Samun Saukin Haihuwa.

Sai a samu ganyen na'a-na'a da garin habbatussauda da garin albabunaji a rinka dafawa da zuma kadan a rinka sha insha Allah za'a samu waraka. 


Matsalar Warin Baki. 

Sai a rinka kuskure baki da wannan hadin za adace da yardar Allah ruwan zafi rabin kofi. Ruwan kai cokali(2) zuma cokali(3) a rinka kurkure baki dashi, sannan kullum a rinka shan zuma da ruwan zafi. 


Ciwon Mara Ga Mata;

Sai a samu garin zaitun da garin habbatussauda a rika dafawa da zuma a rinka sha safe da yamma insha Allah duk matar da take ciwon mara a lokacin al'ada sai tasami man zaitun da na'a na'a da ruwan tsamiya ta rinka sha Insha Allah matsalar ta kau. 


Matsalar Basir Mai Tsiro Ko Marar Tsiro Ko Zafin Dubura. 

Duk mai wannan cutar ko matsalar to sai ya samu man sim-sim da man zurman da man zaitun da man habba sai ya hada su wuri daya a rika shafawa. Sannan a hada garin yansun da garin hulba a tasasa da zuma a rinka sha safe da yamma. 


Amfanin Garin Kuma Soriya. 

Garin kuma soriya shine garin khallown fiya, yana da muhimmanci sosai a bangaren ciwo kamar :

Ulcer

Hawan Jini 

Ciwon Kai 

Da Yawan Zafin Jiki.


 Matsalar Ulcer:

A samu karamin cokalin kumasoriya da na habbatussauda a kadasu da madara(peak milk) rabin gwan-gwani a rinka sha sau biyu a rana za a sha mamaki, sai a godewa Allah, kuma a yi min addu'a


Matsalar Hawan Jini;

A samu gwan-gwanin kumasoriya biyu, na madobiya biyu hanu gwan-gwani daya sai a hadesu a dafasu da ruwan da suka kai kimanin galan daya sai a rinka shan karamin kofin shayi sau biyu a rana za a ga saurin samun waraka da ikon Allah ko kuma a samu man zaitun cokali daya(1) man habiba cokali daya(1) zobo kofi daya(1) sai a rinka sha safe da yamma har sai an samu sauki.


Ciwon Sugar

Dangane da matsalar ciwon suga sai a samu kumasoriya gwan-gwani daya(1) sawunya

gwangwani daya(1) sai kuma a samu yadiya dai-dai kima a hadasu duka sa ruwan da

suka kai kimanin galan daya(1) sai a tafasasu a tace a rinka shan karamin kofi sau

biyu a rana. 


Amfanin Hulba. 

Hulba tana da amfani sannan kuma ta sami babbar shaida daga babban shugaba shine manzo Allah(saw) munsan amfani hulba damun bayarda awo daya kyautar zinari don a bamu hulba saboda amfaninta manzon Allah (saw) yayi gaskiya.


Maganin Kumburin Nono Da Hulba. 

Duk matar da take fama da kumburin nono ko ciwon nono sai ta samu kofi daya(1) Na 'ya'yan hulba sai ta dafa su da zuma bayan ya dahu, sai a saukeshi marar lafiyar ta rinka cin'ya'yan hulbar da safe kafin karin kumallo sannan sai ki rinka shafe nonon da man hulba safe da yamma.


Rashi Ruwan Nono Ga Mai Shayarwa;

Sai ki samu yansun mai kyau sosai da garin habbatussauda da garin hulba na asali, sai ki rinka dafawa da zuma ki rinka sha sau biyu(2) a rana safe da yamma da ikon Allah za ki samu wadataccen ruwan nono mai tsafta ko kuma ki samu garin zaitun da garin hulba da garin albabunaki sai ki rinka Hardawa da zuma da na'a na'a shayi kina tafasawa kina sha sau biyu (2) a rana safe da yamma da ikon Allah za a samu ruwon nono mai kyau mai tsafta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post