Ko kin san cewa zaki iya samun zuciyar namiji da wasu abubuwa kadan?


Mata da yawa sun rasa gane muhimmiyar hanyar da za su bi domin su Mallake namijin da suke so, wasu sun yi fice wajen zuwa gun bokaye da masu tsafi domin a Mallake musu namijin da suke so. 


Sai dai koda an yi dace kin samu mallake namijin to ba zai dauki wani lokaci ba asirin zai karye. Shiyasa a yau na kawo muku wasu hanyoyi da idan mace tana yiwa wanda take so za ta Mallake shi har abada cikin sauki. 


Ga su kamar haka :


1.Ladabi Da Biyayya 

Zaki samu zuciyar namiji da wannan babban makamin wato ladabi da Biyayya, koda zuciyar sa dutse ne muddin kina yi masa ladabi da biyayya zaki samu kan sa, maza na son ladabi da biyayya hakan na kara masu kaunar mace.


2.Hakuri 

Abu ne wanda sai da juriya domin hakuri abu ne sai an jure, musamman zaman tare hakuri shine gaba, dole ne wani abin sai an yi hakuri wani kuma sai anyi magana.


3.Iya Magana 

Kyawawan lafazi yana da kyau mace ki iya magana, ba kowane magana bane ake fadawa Namiji ba.


4.Iya Kwalliya 

Kwalliya na matukar jan hankalin Namiji, ko da mace ke ba kyakkyawa ba ce wannan kwalliyar yana saka ki kiyi kyau, maza na son ganin mata sun iya kwalliya da ado.


5.Girki 

Babban makamin diya mace Kenan, duk kyan ki da wayewar ki idan baki iya girki ba kawata akwai matsala, koyan girki tun kina gida ake yi, da wannan iya girkin shima tsaf zaki samu zuciyar namiji.


6.Son Iyayensa Da Danginsa 

Ba fa namiji mai hankali da zai yarda ki wulakanta masa iyaye ko 'yan uwan sa, duk kuwa son da yake miki ba zai yarda ba muddin yasan hankali sa ya kuma san mutuncin iyayen sa.


wannan bangaren ma mata idan kuka gane zaku samu zuciyar namiji.


7. Soyayya 

Maza na son macen da ta iya soyayya kuma take nuna masu da soyayya ana samun zuciyar namiji domin lokaci kadan sai namiji ya fada son ki.


Duk macen da za ta kiyaye da wadannan abubuwan da muka ambata babu shakka za ta sace Zuciyar namiji kuma sai yadda ta yi dashi. Da fatan mata za'a Kula da wadannan abubuwan. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post