Duk Wani Magidanci Ya Dace Ya Fahimci Wadannan Abubuwan Game Da Matarsa - Android Pols




Ba kawai maza magidanta su karanta kawai ba, yana da kyau kuma a yi amfani da aiki abubuwan da Ku Karanta. Ina so ne maza ma'aurata su yi amfani da darasin domin gayara Zamantakewar aurensu.


Hakan nan kuwa yana da kyau duk wani magidanci ya fahimci cewa, abunda wata macen take so ba shi ne wata macen take son ba.


Sai dai ga wasu abubuwan da ya kamata duk wani magidanci ya sani.

 

1: Duk wata mace tana son mijinta ya kasance shine Jagoran gidansa.


2: Duk wata mace tana son mijinta ya taimaka mata wajen tarbiyan yaransu da suka haifa.


3: Duk wata mace tana son mijinta ya maidata gimbiyarsa wajen girmamawa da mutuntawa.


4: Duk Wata Mace tana son taga mijinta yana shawara da ita.


5: Duk Wata mace tana son ganin mijinta na alfahari da ita.


6: Duk wata mace tana son taga mijinta na alfahari da ita a gaban abokansa da kawayenta.


7: Duk wata mace tana son ganin ta samu kusanci da mijinta.


8: Duk wata mace tana son taga tana samun lokacin yin hira da mijinta.


9: Duk wata mace na son taga mijinta yafi kowa fahimtar ta.


10: Duk wata mace tana son taga soyayyar da mijinta yake yi mata shike motsa mata sha'awa.


Da fatan maza magidanta zasu daure su rika yiwa matansu wadannan abubuwan harma da kari.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post