Canja Sunan Filin Jirgin Saman Kano Zuwa Malam Aminu Kano International Airport a 1983 - Android Pols


A Rana Mai Kamar Ta Yau 9 Ga Watan Mayu 1983, Shugaban Kasar Nijeriya Alhaji Shehu Usmanu Aliyu Shagari Ya Canja Sunan Filin Jirgin saman Kano zuwa Malam Aminu Kano International Airport. 


Filin Jirgin sama a Kano.

Jirgin-sama ya fara zuwa Kano, a tsakanin shekarun 1924 zuwa 1925, Hakan dai ya faru ne a zamanin Sarkin kano Shehu, inda a wancan lokaci a wata Unguwa da ake kira Bamfai da ke Birnin na kano, Jirage guda biyu masu saukar Ungulu suka fara sauka a wannan Fili na Bamfai.


Bayan saukar wadannan Jirage sai turawan Mulkin-Mallaka na wancan lokaci, suka gayyaci Sarkin Kano Usmanu da Hakiman sa, domin su je su ga irin wadannan Jirage, inda suka amsa wannan gayyata, kuma harma suka shiga cikin Jirgin aka dana su. Daga baya sai aka sake sabon filin Jirgin sama kusa da dai inda wancan na da din yake, a dai dai wurin da ake kira Tukurwa, wanda a yanzu za’a iya cewa Katsina Road. Kuma an gina wannan sabon Filin-jirgi a shekarar 1933, lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero, yana da wajen Shekaru 7 a kan karagar Mulki.


Bayan “yan shekaru, sai aka dan dada matsawa kadan, inda ka gina sabon Babban Filin-jirgin sama da ake kira, (Kano International Airport) wanda aka bude a shekarar1954. Kuma Ministan Sadarwa na Najeriya a wancan lokaci, wato Chief K.O.Imbadiwe, shine ya jagoranci bikin budeshi. An gina shine a kan kudi, Fan din Ingila Dubu dari-biyar. A yanzu wannan Babban Filin-jirgin sama, shi ake yi wa lakabi da Malam Aminu Kano International Airport

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post