Binciken Masana: Dalilin Da Yasa Mata Suka Fi Maza Saurin Fushi - Android Pols
Wani sabon bincike na ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a wasu ƙasashe ya gano cewa mata sun fi maza saurin yin fushi a faɗin duniya.


Tahsha Renee na tsaye a cikin ɗakin girkinta shekaru biyu da suka gabata a lokacin da wata matsananciyar damuwa ta yi dirar mikiya a cikin zuciyarta.


''Damuwa ta fi kowanne abu sauƙin shiga tare da samun muhalli a cikin zuciyata''. kamar yadda ta ce.


A lokacin da ake tsaka da annobar korona, takan kwashe mintuna 20 tana zagaye kewayen gidanta inda take tunano abubuwan da suke yawan saka ta yawan fushi.


Nazarin da BBC ta yi wa binciken ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da Gallup ta gudanar a faɗin duniya na cewa mata sun fi maza yawan fushi.


A kowacce shekara ƙungiyar kan gudanar da binciken a kan fiye da mutum 120,000 a faɗin ƙasashe fiye 150.


Inda ake tambayar mutane abubuwan da zukatansu suka fuskanta a ranar da ta gabata.


Idan aka zo ɓangaren abubuwa masu sosa zuciya, batun fushi da baƙin ciki, da damuwa, da kuma ƙunci su ne batutuwan da mata suka fi bayyanawa fiye maza.


Nazarin BBC ya gano cewa tun daga shekarar 2012 mata sun fi maza jin baƙin ciki da ƙunci, duk da cewa tazarar ba mai yawa ba ce.


A ɓangaren fushi da damuwa kuwa, akwai tazara mai yawan gaske.


A shekarar 2012 duka jinsin biyu sun yi kunne doki a fannin fushi da damuwa.


To amma shekara tara bayan nan mata sun zarta maza fushi da damuwa da kashi shida cikin ɗari.


Wannan batu bai zo wa Sarah Harmon - wata ƙwararriyar likita mai lura da tunanin ƙwaƙwalwa a Amurka - da mamaki ba.


A farkon shekarar 2021 ta samu ƙaruwar masu ɗauke da wannan matsala da ke zuwa wajenta neman sharawari.


''Ina da ƙananan yara biyu, dan haka nake aiki daga gida, haƙiƙa akwai ƙaruwar wannan matsala'' in ji ta.


Wani bincike da wata cibiya a Birtaniya ta gudanar a shekarar 2020 a kan kusan uwaye 5,000, ya gano cewa a lokacin kullen korona uwaye ne ke ɗaukar mafi yawan ɗawainiyar iyalai a Ingila.


Wannan dalili ne ya sa suka rage sa'o'in da suke yi a wajen aiki, ko da kuwa sun fi kowa samun albashi mai tsoka a gidan.


A wasu ƙasashe bambanci tsakanin jinsi biyu ya zarta ma'auni na matsakaicin wanda shi ne kashi shida cikin ɗari.


Alal misali a Cambodiya bambancin ya kai kashi 17 cikin ɗari shekarar 2021, yayin da a Indiya da Pakistan bambancin ya kai kashi 12.


Dakta Lakshmi Vijayakumar wata ƙwararriyar likitar ƙwaƙwalwa, ta ce wannan na faruwa ne sakamakon yadda aka samu ƙaruwar matan da suka yi karatu kuma suke aiki, sannan kuma suka tsaya da kafafunsu a waɗanannan ƙasashe.


A cewarta yawan ɗawainiyar da mata ke yi a cikin gida, da kuma yadda suke shan wahala a wajen ayyukansu ko a hanyarsu ta zuwa gida bayan tashi daga wajen ayyukansu ne ke haddasa yawan fushin.


''A kowacce ranar Juma'a da yamma a birnin Chennai na ƙasar Indiya, lokacin da aka tashi daga wajen aiki nakan ga yadda mata ke turereniyar hawa mota domin tafiya gida'', in ji misis Vijayakumar.


Ta ƙara da cewa "Za ka ga maza na hutawa, a shagunan shan shayi, suna shan abin da suka ga dama. Inda kuma za ka ga mata na ta rige-rigen shiga mota a tasoshin motoci da na jiragen ƙasa.


Suna tunanin abin da za su girka. Mata da yawa sukan fara sayayyar kayan miya tun a kan hanyarsu ta zuwa gida''.


A baya ta ce mata ba su fiya fuskantar fushi da damuwa ba, to amma a yanzu lamuran sun sauya. ''A yanzu suna da damar su bayyana abin da ke cikin zukatansu kuma lallai fushi ya fi yawa'', in ji ta.


Shin mata na samun ci-gaba?

Haka kuma binciken ya ƙara gano wasu abubuwa da suka shafi rayuwar matan a ƙasashen da aka gudanar da shi, kamar haka:


Aƙalla rabin matan da aka gudanar da binciken a kansu a kowacce ƙasa sun ce a yanzu suna ganin suna da damar ɗaukar matakin da suke so game da kuɗinsu fiye da shekara 10 baya.


Aƙalla rabin matan a kowacce ƙasa in banda Amurka da Pakistan sun ce a yanzu suna da damar tattauna batutuwan da suka shafi rayuwar aurensu tsakaninsu da mazajensu.


A mafi yawan ƙasashen aƙalla kashi biyu bisa uku na matan da aka gudanar da binciken a kansu, sun ce shafukan sada zumunta na zamani sun taimaka wa rayuwarsu, duk da cewa a Amurka da Birtaniya alƙaluman na ƙasa da kashi 50 cikin 100.


A ƙasashe 12 cikin 15 na ƙasashen da aka gudanar da binciken kashi 40 ko fiye na matan da aka gudanar da binciken a kansu sun ce damar da aka basu ta bayyana yadda suke ji a zukatansu ita ce dama mafi girma da aka taɓa ba su a rayuwarsu cikin shekarar 10 da suka gabata.


Kashi 46 na mata a Amurka suna ganin mata ba sa samun kulawar likitoci domin taimaka musu wajen zubar da ciki kamar yadda yake a shekara 10 da suka gabata

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post