Amfanin Shan Zobo Ga Lafiyar Jiki - Android Pols




Zobo sanannen abin sha ne a Najeriya da sauran kasashen duniya. Zobo yana da dadi sosai kuma yana da amfani kuma wannan shine dalilin da ya sa mutane da yawa ke son shi.  


Yana dauke da wasu sinadarai kamar su bitamin C, calcium, iron, riboflavin da dai sauran su. 


Haka nan yana yin wasu abubuwan ban mamaki ga jikinka idan ka yawaita shan shi saboda yana da fa'idodi masu yawa ga lafiya. Ga wasu daga cikinsu kamar haka:


1. Yana iya sauƙaƙa ciwon Mara a lokacin Jinin Al'ada : 

Yawancin mata, su kan yi fama da ciwon mara lokacin da suke jinin Al'ada. Saboda haka, shan wannan abin sha wato zobo a lokacin haila zai iya taimakawa wajen rage ciwon marar. 


 2. Yana Taimakawa Ma su Fama Da Hawan jini : 

Kamar yadda bincike ya nuna, Zobo yana da matukar tasiri wajen rage wa ko saukar da hauhawar jini saboda yana dauke da wasu sanadarai dake iya saukar da hawan jini.  


3. Zobo Na Taimakawa Masu Ciwon Sugar:

Bincike ya nuna cewa zobo yana taimakawa wajen daidaita sugar a cikin magudanar jini, kuma yana da kyau da muhimmanci ga mutanen dake da haɗarin kamuwa da cututtukan da ke Kama zuciya.


 4. Yana iya magance Cushewar Ciki:

Cushewar ciki na haifarwa jama'a wahala wajen fitar bayan gida wani lokacin kuma mutum kan sami kansa cikinsa ya baci.


Zobo yana dauke da sanadarin fiber mai yawa wanda ke da muhimmanci ga tsarin narkewar abinci sakamakon haka sai ya ke hana cushewar ciki.


 5. Yana Rage Hadarin Kamuwa Da ciwon koda: 

Zobo yana dauke da sinadarin citric acid, tartaric acid wanda ke da matukar amfani ga koda.  


Idan aka yawaita shan Zobo, wadannan sanadarai da aka bayyana a sama wadanda kuma ke cikin zobo za su taimaka wajen gudanar da aikin koda yadda ya kamata sannan kuma sun hana wani ciwon koda da ake kira (kidney stone) da turanci.


 6. Yana Hana Taruwar Kitse (cholesterol)

Masu bincike Sun gano yadda yawan shan Zobo ke iya daidaita wa ko kuma hana taruwar cholesterol a jijiyoyin jini.  


Yana iya yin hakan a sakamakon sanadaran da ke tattare da shi na hypolipidemic da hypoglycemic Properties. Hakan na taimakawa wajen samar wa jiki kyakkyawan cholesterol wato kitse marar Illa a jiki sakamakon haka zai taimaka wa aikin zuciya.


 7. Rigakafin Kamuwa Da Ciwon Daji: 

Zobo na dauke da sinadarin protocatechuic acid wanda wani nau'i ne na sinadarin antioxidant. Hakanan shan wannan abin sha wato zobo yau da kullun na iya jinkirta haɓakar ƙwayoyin cutar dajin kansa.


 8. Yana taimakawa wajen rage kiba: 

Manazarta a fannin cimaka Sun bayyana muhimmancin Zobo dangane da yadda ya ke iya rage yawan adadin sanadarin stach da glukos a jiki wadanda ke haifar da kiba da yawa.  


Da fatan kun ilimantu daga wannan fa'idodi na zobo da yake yi ga lafiyar jikin dan adam. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post