Amfanin Dabino Guda 5 Ga Lafiyar Mu - Android Pols




Bincike da nazarce-nazarce da masana su ka gudanar kan amfanin cimaka ga lafiyar dan adam sun nuna gaskiyar cewa don samun ingantacciyar lafiya, dole ne mu guje wa abinci mai yawan sanadarin suga. 


Sai dai a gefe guda Nazarin ya nuna cewa zakin da dabino ke da shi na haifar da kuzari, wanda kuma ba shi da hadarin da suga ke haddasawa jikin dan adam. 


Yin la'akari da cewa shi dabino na da wasu sinadarai da ke kara wa jikin bil adama da kuzari Shiyasa malamai a fannin abinci mai gina jiki su ka ba da shwarar yawaita amfani da shi. Maimakon yin amfani da kwayoyin da ba a tantance da ingancinsu ba don samun kuzari, yin amfani da dabino a wannan fagen ya fi fa'ida. 


Labari mai dadi shine cewa a yanzu ana samun nau'ikan dabinai dabam-dabam masu ban sha'awa da inganci a cikin fakiti ko mazubi kala-kala.  


Ɗaya daga cikin abubuwan da na fi so dangane da dabino shine yadda ya ke taimaka wa mata masu juna biyu wajen samun sauƙin nakuda. Saboda shi dabino na bai wa mai juna biyu wasu sinadarai da ta ke buƙata, yayin da suke gab da haihuwa.


Ga dalilai guda biyar da manazarta su ka bayyana cewa yawan cin dabino na samar wa da jiki amfani me yawa:


 1. Dabino na samar wa da jiki sinadaran antioxidants. Duk gwaje-gwaje sun nuna cewa dabino tushe ne da sinadarin antioxidants, busasshen dabino, ya ƙunshi nau'ikan antioxidants daban-daban. Yayin da danyen dabino ya ƙunshi anthocyanidins da carotenoids.


Har ila yau dai busasshen dabino ya ƙunshi polyphenols - kamar koren shayi (green tea). Gwaje-gwaje a cikin ilmin sinadarai na abinci sun nuna cewa wadannan sinadarai da aka ambata a sama suna da yawan gaske cikin dabino idan aka kwatanta da sauran nau'ikan abinci.


 2. Dabino na iya taimakawa wajen daidaiton suga. Masu bincike kan ciwon suga sun nuna cewa dabino na ƙunshe da sinadaran glycemic. Wannan yana nufin cewa cin dabino kaɗai, ko tare da abinci, na iya taimakawa masu ciwon suga nau'in-2 wajen sarrafa sugan dake cikin jini da matakan kitse na jini. Ana iya cin dabinon shida zuwa takwas a lokaci ɗaya ba tare da an hada shi da wani kayan abinci ba.


 3. Dabino na iya taimakawa wajen rage hawan jini.Ma'aunin dabino biyar ko shida yana samar da kimanin milligrams 80 na magnesium, wani muhimmin sinadari da ke taimakawa wajen fadada hanyoyin jini.


Bincike ya nuna cewa karawa da miligiram 370 na magnesium na iya kawar ko saukar da hawan jini, sai dai, shan irin wannan adadi mai yawa a lokaci daya yakan haifar da gudawa. Amma dai a sani amfani da dabino hanya ce mai daɗi don ƙara yawan sinadarin magnesium sannu a hankali.


 4. Dabino na dauke da kayan kara kuzari. Kamar yadda mu ka ambata a sama tun da farko cewa dabino na kara kuzari. Kowane dabino na ƙunshi da fiye da milligrams biyu na choline, bitamin B wanda ke cikin acetylcholine, wanda ke sadar da sako ga ƙwaƙwalwa. Wani abin sha'awa shine, yadda dabinon ya kunshi mahimman sinadari da ya ke inganta lafiyar yara da manya waɗanda ke fuskantar kasalar jiki.


 5. Amfani da dabino na taimakawa wajen kara karfin kashi. Bincike ya nuna cewa Busasshen dabino ɗaya yana samar da kusan miligram 140 na potassium, wanda sinadirai ne mai mahimmancin gaske a jikin dan adam. Masana kimiyya sun yi amannar cewa yawan amfani da potassium yana kare yawan kashi ta hanyar rage yawan sinadarin calcium da ke fita ta cikin koda.


Wannan kadan ne daga cikin amfanin da dabino yake dashi ga lafiyar dan adam. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post