Abinda Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (kashi na biyu) - Android Pols




Mutane biyu ne sukayi sanadiyyar yakin da ya barke a Kasar Sudan, kuma Musulmai ne abokan juna na kut da kut.


Na farko sunansa:

General Abdel Fattah al-Burha, shine Shugaban Sojojin Sudan wanda ya jagoranci kifar da mulkin tsohon shugaba Umar Al-Bashir ya haye kujeran mulki


Na biyu sunansa:

Janar Muhammad Hamdan Dagalo (Hemetti), shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine babban Kwamandan rundinar tsaro na agajin gaggawa da ake kira Rapid Support Forces (RSF)


Wanene Dagalo? 

Kamar yadda na fada a sama, yanzu haka Dagalo shine mataimakin Shugaban Kasar Sudan, kuma shine Babban Kwamandan RSF, wato yana rike da matsayi guda biyu a Sudan kenan. 


Rapid Support Forces (RSF) rundinace ta tsaro da aka kafata tun a lokacin yakin basasar da akayi a yankin Dafur na Kasar Sudan, suna aiki da sarrafa makaman yaki kamar sojoji


Janar Muhammad Hamdan Dagalo gawurtaccen dan ta'adda ne, kuma dan tawaye, a lokaci guda kuma dan siyasa, kamar dai misali da a nan Nigeria mu ce Bello Turji, sannan kazamin mai kudi ne na fitar hankali, bincikena ya nuna min cewa a Sudan babu wanda ya kai Dagalo arziki, shine shugaban masu satar zinare na Kasar Sudan, kusan shine yake juya akalar hako zinare na Kasar Sudan, yayi karfin da a Sudan babu wanda ya isa ya nuna masa yatsa tun daga kan shugaban Kasa. 


Saboda ku tabbatar da kudinsa, lokacin da Amerika tasa aka yiwa Shugaba Umar Al-bashir zanga-zanga da tawaye, anyi wata uku a jere babu albashi a Sudan, Dagalo ne ya ara wa Gwamnatin sudan kudi aka biya albashi a fadin Kasar, yana da mayakansa na RSF sama ds guda dubu dari don har sun fi sojojin Kasar yawa,, makamin da yake hannunsu yafi na sojojin Sudan aminci. 


To lokacin da aka fara zanga-zangar da ta kai ga kifar da shugaba Al-bashir, kafin Sojoji su hadu da RSF su hambarar da Al-bashir, shugaba Al-bashir sai yayi wata dabara na siyasa don ya kara karfi, sai ya kira Dagalo ya bashi jagorancin rundinar  RSF, amma haka Dagalo ya zagaya ya hada kai da abokinsa shugaban Sojojin Sudan Janar al-Burhan suka kifar da Gwamnatin Al-bashir, to daga nan ne sai rundinar sojin Sudan da tayi juyin mulki ta bawa Dagalo matsayin mataimakin Shugaban Kasa, saboda suna tsoron zai iya musu juyin mulki suma, domin ya fisu karfi ya fisu kudi. 


Abinda ya haddasa yakin Sudan:

A cikin azumin watan Ramadan da ya gabata, Shugaban mulkin Soji na Kasar Sudan Janar al-Burhan ya kira abokinsa kuma mataimakin Shugaban Kasa sannan babban Kwamandan rundinar RSF Janar Dagalo tattaunawa na musamman, yace masa muna so rundinar RSF ta dawo cikin rundinar sojin Kasar Sudan a zama daya, to shi kuma Dagalo sai yaki amincewa, yace a wani dalili? shine sukace masa ai ba zai yiwu ayi rundinar soji biyu ba, kuma ba zai yiwu ayi shugaban Kasa biyu ba, haka dai suka watse ba tare da fahimtar juna ba. 


Shi kuma Dagalo da ya fahimci Sojin Sudan zasu bashi matsala, daga kammala wannan tattaunawa sai ya fita ya yaje da mayakansa na RSF ya fara karban iko da wasu gurare a Sudan, shi kuma shugaban Kasa Janar al-Burhan kawai sai ya fito ya ayyana RSF a matsayin rundinar 'yan ta'adda, kunga ya halatta zubar da jininsu kenan, to wannan ne babban abinda ya haddasa yakin Sudan a halin yanzu, a cikin sati guda sau uku rundinar RSF na yunkurin yiwa sojojin Sudan juyin mulki wanda ya kai ga gwabza kazamin fada. 


RSF Sunyi kokarin kwace babban filin tashi da saukar jiragen sama na Sudan dake Khartoum to amma Allah bai basu nasara ba, shi kuma al-Burhan sai yayi sauri ya rufe filin jirgin saboda ya san karfin abokin nasa Dagalo, saboda idan RSF suka kwace filin jirgi, wato aka bari jirage suna sauka, to abinda zai faru shine, Dagalo zai samu tallafi daga abokan huldarsa na duniya irinsu Yariman Saudiyyah Muhammad bin Salman, shugaban Kasar Egypt Janar Abdulfatah al-Sisi, shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron, shugaban Kasar Russia Vladimir Putin  da sauransu, musamman saboda ya yiwa Russia alkawari zai bata damar kafa sansanin soji a Sudan, ita kuma Amerika bata so, tana tare da Al Burhan. 


A rubutuna gaba zanyi bayani akan kudaden da ake kashewa a wannan yaki na Sudan, da salon yakin da karfin makamai da barnan da akeyi a Sudan, da kuma inda yakin ya nufa har zuwa lokacin da masana ilmin tsaro suke hasashen za'a iya kawo karshen yakin. 


Muna rokon Allah Ya kare bayinsa a Sudan, Ya sa yakin ya cinye wadanda suka yiwa shugaba Al-bashir zanga-zanga da tawaye. 


Datti Assalafiy

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post