A Rana mai Kamar Ta Yau a Lahadi 22 Ga Watan Afrilu 1990 An yi Yunkurin juyin mulkin a Najeriya, wani yunkuri ne na juyin mulkin da sojoji suka yi a Najeriya a ranar 22 ga Afrilun 1990 a lokacin da wani bangare na hafsoshin Sojin kasar, karkashin jagorancin Manjo Gideon Orkar, sukayi yunkurin hambarar da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida.
Dakarun Sojoji masu Yunkurin juyin mulkin sun kwace gidan rediyon FRCN da ofisoshin sojoji daban-daban a kewayen Legas, ciki har da hedkwatar sojoji da gidan shugaban kasa a Barrack Dodan. Babangida yana wurin lokacin da aka kai hari a barikin amma ya samu nasarar tserewa ta baya, amma Harin Ya Ritsa da ADC din Babangida, Kanar UK Bello an kashe shi.
A cikin jawabin juyin mulkin da Orkar yayi ya kori wasu jihohi biyar na arewacin Najeriya Daga Kasar, ya zargi Babangida da shirin Nada kansa a matsayin shugaban Najeriya Na Mutu ka Raba, ya zargi gwamnatin mulkin soja ta tarayya da mayar da al’ummar Neja Delta saniyar ware da daukacin Kudancin kasar.
A cikin Takarda da ya karantawa al’ummar kasar ta hanyar watsa shirye-shirye kai tsaye da misalin karfe 4 na safiyar ranar 22 ga Afrilu, 1990, ya yi sanarwar korar jihohin Arewa mai nisa daga Najeriya, jihohin sun hada da Bauchi, Borno, Katsina, Kano da Sokoto. Masu fashin baki dai na ganin cewa Wani bangare na dalilin rashin nasarar juyin mulkin shi ne yadda kabilanci da kuma son zuciya da suka rika yadawa a jawabansu na juyin mulkin. hafsoshin sojojin Arewa sun yi gangamin goyon bayan Gwamnatin Tarayya a lokacin da suka gano cewa Wata makarkashiya ce da aka kulla don Wargaza Tarayyar Kasar.
Duk da yake, ana Tsammanin cewa Manjo Gideon Orkar ne ya shirya juyin mulkin, amma a lokacin Aiwatar da shari’ar juyin mulkin na ranar 22 ga Afrilu, 1990 wasu shaidun sun nuna cewa shi dan kanzagi ne kawai ba shi ne asalin wanda ya shirya juyin mulkin ba. Manyan Masu Ruwa da tsaki a shirin juyin mulkin sun hada da Laftanar Kanar Anthony Nyiam, Manjo Saliba Mukoro, Manjo Cyril Obahor a matakin karshe na shirin juyin mulkin ne suka dauki Orkar a cikin shirin. Haka kuma dole a ce hamshakin attajirin dan kasuwa Cif Great Ovedje Ogboru (Wanda Yayi Takarar Gwamna A Jam'iyar APC A Jihar Delta 2019) shi ne babban wanda ya taimaka da kudi don juyin mulkin.
An kama daruruwan mutane da suka hada da wasu fararen hula bayan yunkurin juyin mulkin, adadin wadanda suka mutu a rikicin da ya barke tsakanin dakarun masu Yunkurin juyin mulkin da dakarun gwamnati da kuma aiwatar da hukuncin kisa da aka yi bayan shari’a, ya sanya ta zama Yunkurin juyin Mulki juyin mulki mafi muni a tarihin Najeriya. Orkar da sojoji 41 daga cikin ’yan ta’addar nasa sun yi arangama da dakarun gwamnati bayan An Wargaza shirin Nasu an Kamasu kuma An same su da laifin cin amanar kasa. A ranar 27 ga Yuli 1990, an kashe su ta hanyar harbi.
Ga jerin Sunayen Wadanda Aka Kashe ta Hanyar Harbi
1, Major Gideon Orkar
2, Lieutenant Awokoya E Akogun
3, Captain Nimibibowei Harley Empere
4, Lieutenant Cyril Okuser Ozoalor
5, 2nd Lieutenant Arthur Bandenyintite Umukoro
6, Staff Sergeant Julius Itua
7, Sergeant Martins Ademokhai
8, Sergeant Pius Ilegar
9, Lieutenant Nicholas Odey
10, Captain Perebo Aboela Dakolo
11, WO2 Monday Bayefa
12, Lance Corporal Jephthan Inesai
13, Corporal Sunday Effiong
14, Lance Corporal Francis Ogo
15, Lance Corporal Samuel Mbasue
16, Lance Corporal Albert Ojerongbe
17, Lance Corporal Geofrey Deesiiyira
18, Lance Corporal Emmanuel Aiyemola
19, Sergeant Stephen Iyeke
20, Corporal Joseph Efe
21, WO2 Afolabi Moses
22, Lance Corporal Idowu Azeez
23, Lance Corporal Vitalis Udzer
24, WO2 Jonathan Ekimi
25 Staff Sergeant Solomon Okunbawa
26, Private Richard Isaghohi
27, Staff Sergeant Barnabas Jarikpe
28, Private Egwola Makpamenkun
29, Lance Corporal Adegamen Friday
30, Private Monday Esebawen
31, Private Nnadi Mogaha
32, Sergeant Etim Umoh
33, Ex-Corporal Wasiu Lawal
34, Ex- Lance Corporal Ekominar Makililo
35, Ex- Lance Corporal Peter Umuyoma
36, Ex Sigralman Goodluck Emefe
37, Ex-Staff Sergeant Sampson Idejere
38, Sergeant Jolly Agbodowei
39, Lance Corporal Samuel Obasayi
40, Private Osazuwa Osifo
41, Lance Corporal Goodluck Ofojarere
42, 2nd Lieutenant Emmanuel O Alade
43, 2nd Lieutenant F J Esuku