Yakin Uhud 7 Ga Watan Shawwal Shekaru 3 Bayan Hijra - Android PolsA Rana mai Kamar Ta Yau Asabar 7 Ga Watan Shawwal Na Shekara Ta 3 Bayan Hijra Annabi Muhammad (SAWW) Daga Makkah Zuwa Madina Aka Gwabza Yakin Uhudu. 


Yakin Uhud (Da Larabci:غزوة اُحُد) sanannen Yaki ne na Annabi Muhammad (SAWW) da mushri*kan Makkah a shekara ta 3/625 miladiyya. Kuraishawa sun yi tattaki zuwa Madina, kamar yadda suke so su rama abin da suka yi a yakin Badar. Abu Sufyan shi ne kwamandan rundunar Tasu.


Abubuwan da suka faru a Badar da arangamar da aka yi na tarihi, ya ci gaba da ruruta wutar kiyayya a zukatan Mushr*ikan Makka.


Jagoran shirka da kiyayya da Musulunci na lokacin, wato Abu Sufyanu ba shi da wani tunani in ba na yaki ba, da yadda zai sake kai hari a kan Musulmi da samun nasarar soji da zai sauya irin mummunan Abinda da yakin Badar ya yi musu a ruhi, Don haka sai Mushi*rikai suka kada tambarin yaki, suka shirya keta iyaka da kai hari a kan Madina.


Bangarorin biyu sun hadu ne a wajen dutsen Uhudu da ke gefen Madina. Sai Manzo (SAW) ya aje taswirar yaki, ya shata matsayar sojojinsa, ya sanya wasu maharba a daidai farkon runduna, adadinsu ya kai mayaka hamsin, don su bayar da kariya ta baya ga rundunar Musulmi.


Da farkon wannan yaki dai dukkan alamu suna nuni ne ga nasarar Musulmi, don kuwa dakarun Musulmi sun mamaye fagen fama da kuma wasan kura da makiya, inda suka sami ganima mai yawan gaske.


To amma maimakon musulmi musamman maharban da Manzon Allah (SAWW ya ajiye su su kula da wannan umarni nasa, sai hankula suka koma kan ganima, inda wadannan maharban suka bar wuraren da aka aje su, suka nufi wajen ganima. Wannan ne ya haifar da mummunar baraka a sahun masu jihadi, yayin da Khalid bin Walid, kwamandan Mush*irikai a wancan lokacin, ya yi amfani da wannan dama ya rufarwa mayakan Musulmi ta bayan su. Wannan samame ya haifar da cin karfin rundunar Musulunci da watsewarta, babu wanda ya saura tare da Manzo (SAW) sai Ali bin Abi Dalib (AS), Sayyadina Hamza bin Abdulmudallibi, (RA) Da Mus'ab bin Umair (RA) da wasu 'yan tsiraru daga Sahabbansa, wadanda suka iya kange Manzo Allah (SAWW) da hana kaf*irai isa gare shi.


Raunin ya tsananta, kuma hasarar da aka yi ta yawaita. Musulmi sun yi hasarar Hamza bin Abdulmudallibi (RA) da Mus'ab bin Umair (RA) da wani adadi na Shahidai.


Mutanen Makka sun bi ta kan sojojin musulmi kuma sun yi shahada da yawa, musamman Hamza ibn 'Abd al-Muddalib. Jubair ibn Bawan Mut'im, Wahshi ibn Harb, ya jefi da Hamza da mashi, Yayi Shahada sannan ya farke Cikinsa, ya fitar da hantarsa ​​ya Baiwa Hindu matar Abu Sufyan, Ta ci hantarsa, ​​saboda Hamza ya kashe mahaifinta a baya. Bayan da Hamza ya yi shahada da kuma Farke Cikinsa da Akayi Annabi Muhammad (SAWW) yayi tsananin bacin Rai.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post