Yadda Ake Samun Rayuwa Mai Dadi - Android Pols
1. Karka tsani kowa, duk girman rashin fahimtar ka da yayi, ba wanda yasan mi zai faru tsakanin ku a gobe..!


2. In ka samu ɗaukaka ana so ka rayu cikin saukin kai da sauƙaƙawa cikin mu'amala, ka sani duk irin damar da Allah ya baka da yawan dukiyar da Allah ya baka wani na gaba da kai..


3. Duk halin da ka samu kanka, kayi haƙuri kuma ka yi tunani mai kyau, ka tuna cewa baka da mafita data wuce ka dogara ga Allah, haƙiƙa komawa ga Allah nasa duk ƙuncin rayuwa da kake ciki wata rana zai zama sai labari..


4. Kada ka raina kanka, in ka tashi yin alheri ka bayar da yawa kar ka matse hannu komi ƙarancin abinda kake samu. Ka sani matsin hannu da rowa ba halin muminai bane..


5. Daure ka cigaba da yin Sallama ga wadanda suka juya maka baya suka manta da kai, sannan kayi yafiya ga waɗanda suka ɓata maka. Insha Allahu wata rana za suyi nadamar butulci da muguntar da sukai ta ƙulla maka...


6. Karka daina yin addu'ar alheri ga kanka da waɗanda suke sonka, suke mutumtaka, ka sani kullum kana ransu, kuma in alheri ya same ka suna jin farin ciki ko da basu gaya maka ba.


Ya Allah Ka tsare mana imanin mu da mutumcin mu Ka sa Mu yi kyakkyawan ƙarshe, Ameen Ya Hayyu Ya Qayyumu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post