Zogale ganye ne da aka dade ana yin amfani dashi a kasashen duniya wanda ake sarrafa shi a ci a matsayin abinci ko kuma magani.
Amfanin da Zogale ke yi ga lafiyar jikin dan adam ba zai lissafu ba, amma ga kadan daga cikin muhimman amfanin zogale kamar haka:
1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a
sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).
2- Ana shafa danyen ganyen zogale
akan goshi domin maganin ciwon kai.
3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko
wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen
ganyen zogale insha Allah jinin zai tsaya.
4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya
hada garin
zogale da man zaitun ya shafa.
5- Ana sanya garin zogale akan wani
rauni ko gyambo domin saurin warkewa.
6- Sanya garin zogale a cikin abinci,
yana maganin hawan-jini da kuma karawa mutum kuzari.
7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa
kanwa 'yar kadan domin maganin Ciwon shawara.
8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga
ruwan danyen zogale, haka mai fama da
ciwon kunne.
9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
10-Wanda ke fama da yawan fitsari
wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.
11-Idan aka tafasa furen zogale da
albasa aka sha kamar shayi yana maganin
sanyi.
12-Haka ma cin danyen zogale yana maganin
tsutsar ciki ga yara.
13-Ana daka ganyen zogale da 'ya'yan baure a
sha da nono ko kunu yana maganin
ciwon hanta.
14-Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya 'ya'yan zogale a daka sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
15-A daka zangarniyar zogale da 'ya'yan da ke
ciki tare da kaninfari, citta, masoro
da kuma kimba domin karin karfin da namiji
da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.
16-A daka saiwar zogale da 'ya'yan
kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki
(Apendis).
17-Haka kuma idan mutum yana
fama da ciwon Aids zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.
18-Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai
iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.
Wannan sune daga cikin amfanin da zogale ke yi ga lafiyar jikin dan adam, da fatan kun amfanu.
Ana Bukatar Jama'a su yada wannan Post zuwaga Sauran Al'umma domin Qaruwa da Juna.