Sirrin Dake Cikin Ya'yan Kankana Da Ba kowa Ya San Hakan Ba - Android Pols


Idan ka sha kankana to ka daina jefar da kwallan, maimakon haka sai ka tarasu a waje daya ka wanke ka shanya a rana har su bushe, ko ka siyo wadanda ake siyarwa a herbal medicine store.


Zaka dauki kamar guda 20 zuwa 30 sai ka nike su, har sai sun koma gari (powder).


Sai ka nemi ruwa kamar liter daya da rabi ka zuba garin ka tafasa sai ruwan sun Tafasa. Shikenan hadin ya kammala.


Zaka sha sau daya a kullum amma zaka dakata a duk bayan kwana uku. Idan ka sha na kwana biyu to a ran na uku ba zaka sha ba sai washe gari. A haka zaka rinka yi har zuwa wani lokaci ya danganci ciwon da ake son magancewa da kuma jimawar matsalar a jiki.


Yawan shan wannan hadin na taimakawa wajen magance wadannan cututtuka kamar haka :


1. Domin samun zuciya mai koshin lafiya da rage yawan wasi-wasi.


2. Maganin yawan batun zuci.


3. Karawa garkuwar jiki karfi da kuzari.


4. Samun maniyyi mai rai da maganin karancin haihuwa ga namiji.


5. Gyaran ciki da hanji da wankin dattin ciki.


6. Yana haskaka fatar jiki


7. Domin saurin  warkar da gyambo ko wani rauni a jiki.


8. kariya daga barazanar kamuwa da ciwon Sugar. Idan kana fuskantar wannan barazanar to ka jarraba wannan maganin.


9. Rage nauyin jiki da kiba.


10. Magani ne ga masu fama da anemia.


11. Yana maganin basir mai tsiro.


12.  Rage kumburin hanji, kumburin ciki, kumburin jiki da sauransu.


13. Samun karfi da kuzarin kasusuwan jiki.


14. Yana samar da jini a jiki 


15. Yana wanke koda da sauran datti.


16. Maganin ciwon jiyojin jiki.


17. Yana kare jiki daga barazanar kamuwa da ciwon daji.


18. Yana wargaza tsakuwar koda.


19. Maganin zafin fitsari da toshewar Mara.


Da fatan Allah ya sa za ku yi amfani dashi kamar yadda muka ambata. Allah ya hadamu a ladan gabaki daya amin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post