Sirrin Ayaba Guda 12 Ga Lafiyar Mu - Android Pols



Ayaba na daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi amfani ga jikin dan adam, ayaba na dauke da sinadarin dake karfafa lafiyar jiki. Ga jerin wasu daga cikin amfanin ayaba a jikin dan Adam kamar haka. 


1) Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauki wajen narka abin da aka ci don ta kunshi starch wadda ake samu a cikin Carbohydrates, ba shakka yakan taimaka wajen rage kiba, ta yadda jikkuna za su fara diban wannan starch din a hankali, a sannan mutum zai rika jin cewa ya koshi, sai ya rage gabzar abincin.


2) Ayaba takan sassautar da hauhawar jini, don tana da Potassium, shi kuwa yana da mahimmanci wajen wannan aikin.


3) Zai yi kyau mutum ya sanya Ayaba a matsayin dan abin da zai rika jefawa a baki lokaci zuwa lokaci kafin cin abinci, ya fi mutum ya ci abin da zai kara masa kiba, idan ya ji wata ‘yar kasala sai ya janyo guda ya kada ta a baki ya lakake ta, ta ma fi wasu juice din da suke dauke da Caffeine, musamman yadda ba ta da sukari sosai don dacewa da ci lokaci-lokaci, kamar in mutum yana wajen aiki, ko tarurrukan da kan dauki dogon lokaci, ko ma kallon talabijin.


4) Ayaba takan kusan zama wajibi ko don lafiyar hanji, Ayaba kwaya daya tal za ta iya yi wa matum maganin basir, don tana da wani nau’in Fibres na masamman wanda yake taimaka wa hanji wurin aikinsa, wannan magani halittacce ya fi kara lafiya sama da magungunan bature, masamman wadanda suke da side effect.


5) Banda wannan kuma Ayaba takan sanya kwanciyar hankali da dadin rai, domin tana da sinadarin Tryptophane wanda daya ne daga cikin sinadarorin da suke natsar da mutum da ba shi kwanciyar hankali na hakika, ta daidaita tsarin Protein a jiki, don ba wa mutum cikakkiyar sakewa.


6) In da a ce mutum zai rika cin Ayaba sau uku a rana, wato wajen kari da wurin kalacin rana ko na maraice to Potassium din dake cikinta zai karfafa kwakwalwarsa, don dalibai kuwa yakan fi amfani don yakan kara musu concentration sosai a lokacin daukar darasi.


7) Game da mata masu ciki kuwa Ayabar takan taimaka musu don tana da fa’ida ba karama ba ga mai juna biyu, masamman lokacin da take jin laulayi ko tashin zuciya wanda yake yawan faruwa idan cikin yana karami, sannan Ayabar za ta iya taimaka musu wajen ganin Glucose dake cikin jininsu bai nemi karuwa ba, takan kuma lura da yanayin zafin jiki.


8) Sai kuma zancen cizon sauro, wani in sauro ya cije shi sai ka ga wurin ya yi hulu-hulu, to a irin wannan yanayin za a iya bare Ayaba a sanya bawon a wurin, don yakan magance kaikayin da wurin yakan yi, shi ma wannan ya fi aminci sama da magungunan da mutum zai yi ta shafawa.


9) Ayaba takan taimaka kuma wajen magance Ulcer, ko kuma riga-kafin hakan, domin takan taimaka wajen kankanta Acid din da abinci yakan bari a tumbi, ta wajen daidai ta acids narka abincin, da wannan sai ka ga ta yi maganin matsalolin tumbi da dama.


10) Ayaba tana da Iron sosai ga wadanda suke da cutar fatarar jini ko Anaemia, don Iron din kan taimaka musamman ga kwayoyin jan jini wanda yake kula da dauko Oxygen, ya kuma tabbatar da cewa ruwan jiki wato white blood ya ba da gudummuwarsa wajen magance raunuka.


11) Wani abin mamaki Ayaba hatta a gona bawonta yana da amfani, don kuwa takan zama taki idan aka kai ta can, kenan a maimakon a rika zubarwa gwara a kai shi can inda za a yi aiki da shi don abincin da za mu ci.


12) Ayaba takan taimaka sosai wajen kiyaye lafiyar koda, ta yadda take kankanta tura Calcium zuwa fitsari, da karanta yuwuwar kamuwa da tsakuwar koda, kamar yadda bincike ya gano cewa cin Ayaba yakan rage hatsarin kamuwa da kansar koda, ta yadda aka sami mata wadan da suke cin Ayaba sau 4-6 a sati yadda suka nesanta da kamuwa da kansar koda sama da wadan da ba sa ci, ban da wannan ma sinadarori masu dama da suke cikin Ayaba sun sanya tana iya kawar da matsalar Ulcer kai tsaye.


Galibin Ayaba har da karkasuwar nau’o’inta duk tana dauke da sinadarori kala daban-daban, akwai ma doguwar Ayaba wacce yawan cinta Inyamurai muke ganin suna sayar da ita, ba a iya cinta sai an soya, ko kuma a gasa ta a wuta, mukan ga ana sanya ta ne a abinci kamar shinkafa, sai a yanyanka ta a dora ta a sama, sunanta Plantain, sukan kira ta da Larabci “Mauzul Janna” ita wannan Ayaba tana da starch sosan gaske, kuma ba ta da sukari mai dama, ita ma tana da tasiri wajen kawar da maiko a cikin jini, a taqaice dai ita ma ayaba ce.


Wallahu a'alamu


Wannan sune wasu daga cikin amfanin da ayaba ke yi ga lafiyar jikin dan adam wanda ba kowane yasan hakan ba. Da fatan kun karu daga abinda kuka Karanta kuma daga fatan za ku turawa sauran al'umma domin su amfana. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post