Rayuwar Matan Aure: Ko kunsan Akwai Matan Auren Da Ba Su Da Bambanci Da Gwauraye?Tabbas cikin matan aure ma akwai Gwauraye, bambancinsu da mata gwawraye shine su suna da mazan da aka daura masu aure tare kuma suna zaune a gidajensu da sunan zaman aure kuma mazan na kula da cinsu da lafiyansu amma zance na jima'i duk daya suke da mata gwagware marasa mazan aure.


Muddin hirar matan aure ya haura mintuna goma, to tabbas sai kaji an tabo magana rashin wadatar jima'i ga wadannan matan ko kuma ga wata kawarsu, ko kanwarsu ko kuma ma 'yar da suka haifa, wanda wannan matsala a kullum sai kara karuwa yake yi kuma har yau din nan magidanta da damar gaske basu da tunanin yadda zasu kawo karshen wannan lamarin.  


Wannan matsala da matan aure gwawraye suke fuskanta bai tsaya kawai akan matan talakawa ba wadanda ake ganin cewa rashin wadata ne da neman abunda zasu ci da iyalansu yasa basu samun cikenken lokacin da zasu gamsar da iyalansu a jima'ince. 


Zaka sha mamaki idan ka ji yadda matan masu kudi, masu mulki, matan manyan ma'aikatan gwamnati, matan 'yan sisaya dama matan sarakuna suke kokawa da yadda mazansu suke barinsu cikin matsalar rashin samun wadatatcen kuma gamsancen jima'i a matsayinsu na mazajensu kuma wadanda sune kawai Allah ya yardar masu da su kusancesu kuma su kwantar masu da sha'awa ta kwanciyar aure a lokacin da bukatar hakan ta taso musu.


Ana samu wasu mazan da koda yaushe su akan hanya suke a kullum, wanda hakan yasa basu da lokaci sosai na kasancewa da iyalansu, idan ma sun samu lokacin basu iya gamsar da matan nasu a lokacin da suka tinkaresu da jima'i.


Wasu mazan kuwa yanayin aikinsu ko sana'arsu ya sa basu zaune gari daya da matansu, wadan hakan yasa sai lokaci-lokaci suke samu zuwa gida domin suga iyalan nasu kuma su dan murzasu sama-sama sai kuma su kama hanya suyi komawarsu su ci gaba da harkar gabansu.


Duk da yake wasu malamai na musulunci na gani cewa mace na iya daukar tsawon watanni hudu ba tare da jima'i ba wanda kuma hakan ya zama wata hujja ga wasu mazan ina ganin cewa wannan hujja bai zama ka'ida ba ga dukkanni mata ba.


Kamar yadda malamai na jima'i suka nuna, ba kowace mace bace zata iya hakurin wata hudu ba sabis ba, haka kuma wata ko wata guda bazata iya ba, wata ma ko da sati daya bata iya wa, da a kwai wasu matan ma ko hakurin rana daya ba zasu iya ba muddin dai da ransu da kuma lafiyansu. 


Idan kuwa haka ne babu wata hujja ga wani magidanci da haka kawai saboda wata hujja nasa ko son rai irin nasa yayi watsi da matarsa ya barta tana ta rungumar filo idan mai tsaron Allah ce shi kuma yana can yanata shagalinsa da wasu matan maza nawa ne suke iya hakurin tsawon lokacin da matansu suke hakuri ba tare da sun nemi matan banza ba?


Bama wannan ba. Akwai mazan duk da basu da lokacin mace guda. Ko basu da lafiya ko karfin iya yin jima'i da mace fiye da guda, ko kuma yawan shekaru. Amma zaka gan su da mata fiye da guda wasu ma har hudu suke aurowa amma su kasa iya gamsar da su.


Wannan damar dana samu na rubuce-rubuce da nake yi ya bani damar kusantar mata da dama, cikinsu dama matan aure. Hakan yasa na fahimci irin halin da irin wadannan matan suke ciki na kunci da hakuri, rashin samun wadatar jima'i da mazaje su a matsayin su na matan aure.


Wasu cikinsu suna iya hakura sun kuma daurewa ransu. Wasu kuwa wannan yasa suke neman saki wajen mazajen nasu duk kuwa da suna son zaman auren. Wasu kuwa masu aurensu daban masu biya musu bukata kuma daban a hakan suke zaman auren.


Akwai kuma mazan da su ba wai jima'i bane basa yi da matan ba. Amma Sam basa iya gamsar dasu a lokutan jima'i don haka matan suna rayuwa ne a gidan mazajen tamkar marasa aure idan dai ta fannin jima'i ne.


Yanada da kyau maza mu tausaya wa matan da muke aure wajen sauke wannan nauyin na gamsar dasu. Ka iya sani yadda bazaka iya hakurin zama baka yi ba haka ita ma bazata iya ba. Yadda kake son ka samu gamsuwa a lokacin da kayi haka ma ita ma mace take bukatan gamsuwa idan anyi.


Yana da kyau ka sani, ita mace tamkar gona ce sai da zagaye ana ban ruwa, idan kai kaƙi bata ruwa kila maƙocinka na iya badawa ko wani can da yake da sha'awar taimakamaka wajen ban ruwa. Don haka sai mu kiyaye.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post