Kanal Muhammadu Buhari Shugaban Farko Na Kamfanin NNPC 1977 - Android PolsA Rana Mai Kamar Ta Yau 29 Ga Watan Afrilu 1977 Shugaban Kasar Nijeriya A Mulkin Soja Janar Olusegun Obasanjo Ya Nada Misnistan Man Fetur Na Najeriya Kanar Muhammadu Buhari A Matsayin Shugaban Kamfanin Man Fetur Na Kasa NNPC Kuma Na Farko Tun Kirkiro Da Kamfanin A Ranar 1 Ga Watan Afrilu A Shekarar. 


A shekarar 1977, lokacin da aka kafa kamfanin man fetur na Najeriya, Buhari ya zama shugaban Kamfanin inda ya rike har zuwa 1978. A lokacin da yake rike da mukamin ministan man fetur na tarayya, Haka Kuma Gwamnati ta zuba jari a fannin Matatun mai.


Najeriya ta shiga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) a shekarar 1971, ta kuma kafa kamfanin man fetur na kasa (NNPC) a shekarar 1977.


Kamfanin Man Fetur na Najeriya ko kuma kamar yadda muke kiransa kawai, NNPC kamfanin mai da iskar gas ne na Najeriya. An kirkiro Shi ne Bayan An Rushe Hukumar hadakar kamfanin mai na Najeriya, ko NNOC, da ma’aikatar ma’adinai da karafa ta tarayya. Ta hanyar doka mai lamba №33, ta mallaki hakki da kadarorin hukumar ta NNOC tare da daukar nauyin wasu ayyuka na ma’aikatar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post