Jerin Kalolin Abinci Da Cin Su Ke Karawa Mata Ni'ima Da Sha'awa A Zamantakewar Aure - Android Pols




Mata da yawa na korafin rashin sha'awa dake damunsu wanda ke jawo musu samun sabani da mazajensu. 


Duk matar da ta san tana da irin wannan matsalar ta rashin sha'awa da ni'ima to ga wani sirrin da na kawo muku wanda zai taimaka muku dawo da maratabarku na mata. 


Ga nau'in abincin da za ki rika ci idan kina son karin ni'ima da sha'awa kamar haka :


1. Gyada.

Masanan sun tabbatar da cewa gyada na kunshe da wani sinadari da ake kira "amino acid L arginine" wadda ke taimakawa wajen bunkasa sha'awar mace.


Haka nan sun bayyana gyadar dai tana taka muhimmiyar rawa wajen hana bushewar al'aurar mata. Idan haka ne kuwa ba makawa za ta karawa mace ni'ima, sannan a gefe guda ta kara mata karfin sha'awa.


2. Tafarnuwa. 

Tafarnuwa na da wani sinadari da ake kiran sa "allicin" da turanci. Aikin wannan sinadari shine taimakawa wajen harba jini zuwa kwakwalwa da dukkan sassan jikinmu, ke nan har da al'aurar mace. Wanna aiki da take a jikin dan adam, sakamakon wannan sinadari ya sa tafarnuwa ta kasance ta gaba-gaba wajen motsa sha'wa ga mata.


Ko da yake wasu ba sa son amfani da tafarnuwa saboda warinta, to idan kin kasance daya daga cikin su, sai ki nemi manta, ko kafsonta don kuwa akwai su a kasuwa a mazubi nau'i dabam-dabam.


3. Burokoli (Broccoli)

Wannan wani nau'in kayan lambu ne da ke da matukar fa'ida kwarai da gaske wajen motsa sha'awa da ni'imar mace.


Me ya sa burokoli ke wannan aiki a jiki? Masanan sun tabbatar da cewa yana kunshe da sinadarin bitamin C mai yawan gaske. Shi kuma sinadarin na bitamin C, na taimakawa wajen kewayawar jini a jiki sannan ya gyara hanyoyin jinin. don haka a lokacin da aka fara gabatar da wasa kafin jima'i tuni jini zai kwarara zuwa ga al'aurar mace. Hakan kuma na motsa sha'awarta sannan ta samu damar gamsar da miji.


4. Kwai

Shi kuwa kwai ba iya motsa sha'awa da kara ni'ima ga mata kawai ya ke yi ba, a'a masanan sun ce ana iya maganin raunin mazakutar namiji da shi, sannan ana amfani da shi wajen magance larurar rashin haihuwa. Ta wajen kara yawan maniyyi da kuma ingancinsa.


Duba da irin amfanin kwai a garemu, hakika ko ba'a fada ba, ke kin san yawaita amfani da shi zai motsa sha'awarki sannan ya kara miki ni'ima yadda za ki gamsar da mai gida.


Akwai wani sanadari da ake kiran sa "bitamin B complex" a cikin kwai da ya ke karawa mutum walwala da inganta yanayin jima'i.


Wasu masana sun bada shawarar amfani da danyen sa ga wanda zai iya, ko kuma soya shi sama-sama, ko hada danyen sa da madarar ruwa a gauraya a shanye.


5. Hanta.

Ko ba'a fada ba mai karatu ya san hanta na kunshe da sinadarai masu gina jiki. Hakan ya sa yawaita amfani da ita ke inganta lafiyar mace, ya kara mata ni'ima. Idan kuwa haka ta kasance ka ga da zarar mai gida ya ce kule yanzu uwar gida ta ce masa cas.


Anfi son a soya ta ko a dafa amma sama-sama. a hada ta da albasa da sauran kayan hadi da uwar-gida ko amarya za ta ji dadin cin ta.


6.Yayan Kabewa.

Yayan kabewa na kunshe da sinadarin "zinc" da nau'ika dabam-dabam na bitamin da suka hada da Bitamin B,E,C,D da K ga kuma sinadaran "niacin, calcium, potassium wadanda suke taimakawa mace wajen tayar da sha'awarta da inganta mata ni'ima.


7. Dankalin Gida.

Shi kuwa yana kunshe ne da sinadarin "potassium" da wasu sinadarai da su ke inganta ni'imar mace da kuma kara mata sha'awa.


8. Kayan Marmari Da Na Lambu.

Wani bincike da aka gudanar kuma aka wallafa a mujallar "International Journal of impotence research, a shekara ta 2007", ya nuna matan da su ke yawaita cin kayan marmari da na lambu musamman ganyayyaki sun fi takwarorinsu da ba sa yawaita cin dangogin wadannan abinci ingantacciyar lafiya, karfin sha'awa da kuma ni'imar gamsar da mai-gida.


9. Kankana.

Kankana na daya daga cikin dangin abinci mai kara ni'ima da sha'awa ga ya mace. Ba komai ya sa ta wannan aiki ba sai wani sinadari da ke taimakawa wajen tausasa hanyoyin jini, hakan kuma sai ya bayu wajen gudanuwar jinin zuwa ga sassan jiki har da al'aurar mace. Hakanan kankanar ta ke kara ni'ima ga mace.


Don haka a yayinda abu biyun nan suka hadu, to fa uwar gida ba sai an fada ba.


Ana son a sha kankana mintuna 30 kafin jima'i, kuma idan ana son samun cikakken aikinta sai a cinye harda wannan farar tsokar bayan an shaye gurin zakin ke nan. Abin da yasa muka ce haka shine, masana sun tabbatar da cewa, shi wannan sinadarin ya fi yawa a cikin farar tsokar, koma bayan wannan jan, me zakin.


10. Dabino.

Dabino yana da matukar amfani ga rayuwar ma'aurata. Amfaninsa bai tsaya ga iya mace ba, har da shi namijin.


Binciken da masana suka gudanar akan dabino ya bayyana cewa yana kunshe da sinadarai da ke kara yawan maniyyi da kuma ingancin sa.


Ba karin sha'awa ba kadai, ana iya amfani da dabino don gusar da matsalar raunin mazakuta ga maza.


Hakanan sun kara da cewa yana da wasu sinadarai da ke karawa namiji kuzari ita kuma mace ya kara mata girman nono.


Da suke bayyana yadda za'a fi cin gajiyar aikinsa, sun ce a jika kamar guda 7 ko 8 a ruwa a bar su tsawon awa 3 sannan a ci. Da fatan za'a juri yin hakan.


11. Zuma.

Tun shekaru da yawa da suka wuce mutane ke amfani da zuma don inganta rayuwar aure. Hakazalika a wannan zamani da muke ciki ana iya amfani da zuma don samun wannan fa'ida.


Zuma na da wani sinadari da ake kiran sa "boron" wanda ke sarrafa wasu sinadaran halitta a jikin mace da ake kiran sa "estrogen" da shi kuma ya ke saurin motsa sha'awrta.


Wadanna su ne nau'ikan abinci guda goma sha daya da muka zakulo muku don inganta rayuwar aure tsakanin ma'aurata.


Kuma a kullum muna jan hankali cewa. ba dole ne a hada dukkanin wadannan dangin abinci ba, a'a za'a zabi wanda aka ga za'a iya ne kuma ya fi saukin samuwa ga mutum, Allah Ya sa mu dace, amin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post