Domin Ma'aurata: Yanayin sha'awar mace da namiji akwai bambanci - Android Pols


Ku maza sha'awa da so abubuwa biyu ne da kuke iya banbancewa, shiyasa ko da bakwa son mace za ku iya saduwa da ita har ku samu yadda kuke so. Shiyasa kuke iya biyan mace kudi dan ku biya bukatar ku ko da kuwa bakusanta ba. 


Shiyasa za ku iya kasancewa cikin fushi da mace ko kuna fada da iyalin ku bazai hana ku biyo dare da bukatar kuba dan ita sha'awar ku da abinda ke zuciyar ku basa haduwa. 


Ita kuma mace.


Sha'awarta yana tafiya da son da ta ke yi ma mutum ne, natsuwarta da kai a zuciyarta gwargwadon jin dadin da za ka samu a kan shimfida. Shiyasa yakanyi matukar wuya mace in bata son mutum ta kusance shi, asalima kyamar sa take yi komin tsabtar sa. 


Shiyasa ko fushi tayi da miji za ta iya kaurace masa, balle in kuna da matsaloli tsakanin ku da baku magance shi ba zai yi matukar wuya kaji dadinta a shimfida, wasu shiyasa suke baku hakkin ku amma zuciyar su ya kaurace muku. 


Shiyasa ko da za ka kusanceta cikin jin dadi ta amince, wani abu kalilan za ka yi, ko ka taba wani wajen da ba ta so ya kawar mata da sha'awarta wata har ta iya hakurin ayi domin ita zuciyarta yana da alaka da sha'awarta.  


Shiyasa mafi saukin abinda mace za ta yi idan tana sonka shine ta nemi kusantarka misali rike hannu, hugging, kiss da sauransu cikin sauki da aminci. 


Don haka ina Kira gare ku maza, matukar har kuna son ku ji dadin mu'amalantar iyalanku a shimfida sai kun fahimci yanayin zuciya, jiki da sha'awar mace da inda suka yi tarayya.  


Wannan zai baku damar juyasu da samun su yadda kuke so, wadda ita da kanta za tana bukatarka ko guiding dinka cikin sauki yadda take so.  


Da fatan wannan yar tunasarwa za ta amfanar damu ta hanyoyin da suka dace. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post