Dalilin da yasa baka jin dadin jima'i, mace ko namiji - Android Pols



Matsalar Rashin jin dadi a lokacin Jima'i, ko rashin gamsarwa yana iya faruwa akan namiji da mace. 


Rashin jin dadin jima'i ko rashin gamsar wa yayin saduwa ko rashin jin sha'awa yayin saduwa wanda ake kira da sexual disorder, matsala ce wacce take kasancewa mutum baya jin dadin jima'i, hakan yana faruwa game mace da namiji akan samu daya daga ciki yaji baya jindadin gamsuwa.


Kadan daga cikin abubuwan da suke jawo wannan matsala akwai.


1. Tilastawa yayin Jima'i, mutum baya ra'ayin yayi jimai a matsa masa Dole sai yayi. Wannan yana daga cikin dalilin rashin jindadi a yayin Jima'i, shi Jima'i ana yinsa ne lokacin da ake so hakan yake sa aji dadi da gamsuwa. Amma Idan ana aka ba tare da rai na so ba babu wani dadi da za'a ji. 


2. Matsalolin kwakwalwa, kamar gajiya, damuwa, bacin rai da sauran su. Idan mace ko namiji suna cikin damuwa ko kuma gajiyar wani aiki Jima'i baya yin dadi. 


3. Matsalar ciwon sugar. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa ciwon sugar yakan ragewa mace ko namiji sha'awar son Jima'i. 


4. Matsalolin ciwon zuciya. Masu fama da matsalar Ciwon zuciya galibi Jima'i bai dame su ba. 


5. Shaye-shayen kwayoyi, masu yin ta'ammali da kayan maye basa damuwa da yin Jima'i, domin yana rage musu sha'awar yin hakan. 


6. Yawan shan giya. Shima yana daga cikin abinda ke haddasa rashin jindadin Jima'i. 


Baya ga wadannan abubuwa 6 da suke haddasa rashin sha'awa da jindadin Jima'i akwai kuma abubuwan da suke bayyana kana da matsalar sexual disorder (rashin gamsarwa ko jin dadin jimai) kamar haka :


1. Karancin sha'awa ko rashin Sha'awa baki daya.


2. Rashin motsawar Sha'awa, zaka ji kana son jima'i a zuciyar ka amma kuma zaka ji a jikin ka babu wannan yanayin.


3. Rashin yin inzali lokacin saduwa; shine koda awa nawa za ai ana Jima'i, baza a kawo ba ko a gamsu ba.


4. Jin zafi lokacin jima'i; Masana sun bayyana cewa rashin sha'awa ga namiji yana iya faruwa Sanadiyyar karancin hormones wanda ake kira da testosterone wannan hormones shine yake bayar da sha'awa da kuzari hatta bangaren samar da ruwan maniyyi.


Ta bangaren mace kuma takan samu wannan matsala idan tana da hormonal inblance ko tana lokacin shayawarwa, ko lokacin da mace ta daina ovulation(samar da kwan halitta) da kuma daina ganin al'adar ta.


Haka kuma baya ga wadnnan matsaloli da muka lissafa akwai cutuka dake jawo hakan kamar su:


1 Hawan jini

2 Ciwon zuciya

3 Kwayoyi

4 Yawan gajiya

5 Damuwa

6 Matsalar a zamantakewar aure


Suna iya jawo wannan matsala da rashi ko daukewar sha'awa baki daya.


Saboda haka domin magance wannan matsala dole ne mutum ya ziyarci likita ta yadda za'a gane ainihin abinda yake damun sa sannan a bada magani ko shawarwari.


Allah yasa ku dace 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post