Boko Haram Ta Kai Mumnunan Hari Tare Da Kashe Mutum 10 A Wani Yanki Da ISWAP Ta Ke Da Iko A Borno



’Yan ta’addan kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram, sun kashe mutum 10 a wani yanki da takwarorinsu na ISWAP suka mamaye a Jihar Borno.


Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, mayakan sun kashe fararen hular ne a yankin da ISWAP ta kafa sansanoni a kusa da garin Gashigar da ke iyaka da Jamhuriyyar Nijar.


An tattaro cewa wasu mayakan na Boko Haram haye a kan babura bakwai kuma kowannensu dauke da mayaka uku, sun kai hari a kan iyakar Najeriya da Nijar ta bangaren Gashigar.


Bayanai sun ce mazauna yankin na bayar da hadin kai galibi ga ’yan ta’addar ISWAP da suka yi matsugunni a yankin.


Kwararre kan sha’anin tsaro da tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ya ce, mayakan sun kuma kama wata mota mai dauke da bindiga guda daya da babura shida na ISWAP.


Kazalika, Makama ya ce mayakan na Boko Haram sun kone gidaje da dama a kauyen yayin da na ISWAP din suka ranta a na kare.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post