Ɗan jarida ya murɗe hannun barawon waya ya kuma kwace sharbebiyar wukar hannun sa - Android Pols


A daren Litinin da misalin karfe takwas da minti goma wani ɗan jarida ma'aikacin gidan Radio Kano kuma mamba a kungiyar 'Yanjaridu marubuta labarin wasanni ta kasa reshen jihar Kano, mai Suna Yusuf A. Yusuf Giginyu ya gamu da wasu ɓata gari akan hanyar sa ta komawa gida daga wajen aiki, inda suka tare shi domin kwace wayar hannun sa, amma cikin ikon Allah-Allah ya bashi damar kwace sharbebiyar wukar hannun su, sai dai tuni sun gudu da wayarsa ta hannu kirar Android.


A dan haka Yusuf A Yusuf ke kira ga al'umma da su dinga kula sosai idan suka hango matasa su biyu a kan babur sun nufo garesu da nufin tambayar wani wuri.


Yanzu haka dai Yusuf A. Yusuf yana nan cikin koshin lafiya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post