Alamomin da za ki Gane Namiji na Matukar Sonki ba tare da ya Furta Miki ba - Android PolsAkwai wasu mazan da ba sa iya tunkarar mace gaba da gaba su furta mata kalmar so. Ko kuma su fito fili su nuna wa mace su na sonta.


Sai dai su yi ta yin wasu halaye ko dabi'un da mace idan mai hankaki ce za ta fahimci mai yi mata wadannan abubuwan sonta ya ke yi.


Ga wasu manyan alamomin da mace za ta iya fahimtar namiji ya na sonta ba tare da ya furta mata ba :


1: Na kusa da shi na sonki: Za ki ga abokansa da 'yan uwansa sun jawo ki a jiki. 


2: Za ki ga ya na baki lokaci: Duk namijin da ya ke baki lokacinsa a duk lokacin da kika bukaci hakan tabbas ya na sonki ne.


3: Son abinda ki ke so: Idan namiji ra'ayinku ya na zuwa daya ya na son abinda ki ke so kuma ya na kin abinda ki ke ki akwai alamun ya na sonki amma ya kasa furta miki.


4:Yawan yi miki kyauta: Za ki ga ya na miki kyauta musamman da abinda ya san kin fi so ko sha'awa.


5: Ya na yawan satar kallonki: Idan namiji yana ra'ayinki duk Inda kika shiga idanuwansa na kanki. 


6: Ya na kokarin ganin ya birgeki: Idan namiji na sonki zai dinga yin kokarin miki gwaninta ko da kuwa da kalmominsa ne.


Wadannan sune alamu 6 da mata za su iya gane namijin da ya ke son su amma ya kasa bayyana musu, sai dai ke idan kin fahimci hakan sai ki yi kokarin ankarar dashi yadda zai fito fili ya bayyana miki. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post