Alama 10 Na Balagar 'Ya Mace kashi Biyu - Android Pols



Mace tana balaga ne a shari'ar Musulunci a sadda ta kai shekaru 9 zuwa sama har 15  a lokacin tana samun wadansu canje-canje a tattare da ita.


A yayin da mace ta balaga akwai wadansu alamomi da za ta gani a tattare da ita wadanda suke bayyana cewa yanzu hukumce-hukumcen shari'a sun hau kanta ga su kamar haka:-


1. Fara jinin haila, Zuwan jinin al'ada yana faruwa ne a sadda mace ta kai shekaru 9,10,11,12,13,14,15 amma yanayin wadatar rayuwa jin dadi kwanciyar hankali yana sanya mace ta fara jinin da wuri koma bayan yara mata da suke cikin rashin ababen more rayuwa, ko kunci da tashin hankali.


2. Tsayinta, kaurinta,da nauyinta za su qaru. Za'a ga alamar jikinta ya canja ta kara tsayi da karin jiki. 


3. Fatar jikinta za ta qara kyau da qyalli. Yawanci mace tana yin haske wanda alama ce dake nuna ta girma. 


4. Sannan ita ma kananan kuraje za su rika bayyana a jikinta. Amma ba duka mata ne suke yin hakan babu. 


5. Gabobinta za su girma tattare da zama na manyan mutane. Musamman gabobin hannunta za su yi kauri. 


6. Gashin mara wanda ba karfi zai fito a gabanta da hammatar ta da kafafunta (duk da akwai bambance-banbamce tsakanin wata da wata.


7. Mamanta za su girma (nonuwa) da kuma tsayi, sannan fatar kan Maman nata za ta yi baki.


8. Kofofin zufa za ta bude ta yadda da zarar ta yi wani aiki, jikinta zai rika wari, musamman warin hammata.


9.Mahaifarta za ta girma ta kuma yi tsayi.


10.Muryarta za ta zamanto siririya (cenjin murya).


Wannan sune daga cikin manyan alamu na zahiri da suke bayyana a yayin da mace ta balaga. Sai dai kowace mace da irin nata alamar da suka fi bayyana. 


Za mu ci gaba in sha ALLAHU.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post