Abubuwan Da Mata Za Su Sha Don Karawa Jikisnu Kololuwar Ni’ima - Android Pols



Shan ko wane ruwa daga cikin wadannan ya na saukarwa da mace ni’ima mai kyau, mai kauri da yauki irin wacce maza su ke so, kuma ko wanne ruwa akwai yadda a ke sarrafa shi da mahadan da za su sa mai gida sambatun dadi.


Ga kadan daga cikin yadda a ke sarrafa wasu ruwan daga cikinsu:


1) Ruwan Kankana, A samu yaba manya guda uku, Kankana rabi da Tuffa: Ki hada ki markada ki zuba madarar ruwa gwangwani daya, zuma yadda ki ke so, ki sa kankara ya yi sanyi, ku sha kamar juice ke da maigida. Ya na karin ni’ima da kaurin maniyyi.


2) Ruwan Tumatir: Ki markada tumatir biyu, ki zuba ruwan a cikin kwai uku, ki sa magi da albasa ki soya ya yi ruwa-ruwa ki ci. Shi ma ya na saukar da ni’ima sosai da saka jin dadin auratayya, sannan hakan ya na saka gogewar fata.


3) Ruwan Kwakwa: Ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki goga kwakwar da ‘greater’, sannan ki markada a ‘blander’, sai ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar ki tace ruwan ki fidda dusar. Da ma kin bare dabinonki cikin gwangwanin madarar ruwa daya.


 Ki jika dabinon ya yi laushi sai ki markada ya yi laushi sosai, sai ki zuba a kan ruwan kwakwar, sannan ki zuba ruwan da ki ka fasa kwakwar ya zubo a ciki. Ki zuba zuma da garin madara cokali uku a ciki, ki juya sosai. Ki sa a firij ya yi sanyi ko ki saka kankara. Idan ba ki son sanyi sai ki sha a haka. Ki yini ki na sha; kar ki barshi ya kwana. Hmmm zumdum! Ba zan ce komai ba, sai kin gwada kawai, uwargida za ki ban labari.


4) Ruwan Zogale: Amfanin ruwan Zogale ba zai lissafu ba a maganin cututtukan da ya ke yi ma na a jikinmu. Amma zan yi bayanin amfaninsa a bangaren karin ni’ima a jikkunanmu ne kawai.


Ki tsinke zogale ki wanke ki tafasa sosai ki tace ruwan zogalen ki zuba kaninfari da citta ki tafasa. Sai ki sauke ki dinga kurba da zafinsa kamar shayi. Ya na gyara jiki ya saukar da ni’ima sosai. Ya na karawa mace kuzari a jikinta sosai. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post