Abubuwan Da Ke Sa Mace Ta Fita Daga Zuciyar Mijinta - Android PolsMata da dama suna aikata wasu Kura-kurai wanda ke jawo soyayyar da mijinsu ke yi masu ta dusashe a ransa. Sai dai ba duk mata ne suke lura da kiyaye irin wadannan abubuwan da suke aikatawa ba. 


Hakan yasa a wannan bidiyon muka kawo muku abubuwan da mata suke yi wanda ke jawo soyayyar da mazajensu ke yi musu ta dusashe gabaki daya. Ga dai jerin Abubuwan kamar haka. 


1. Riko 

Riko shine idan an aikatama wani laifi kabar abin a ranka ba tare da ka yafe ba uwargida ta riki maigida a zuci sakamakon wani abu ko maigida yana sa ta fita daga zuciyar miji duk kuwa da irin son da namiji yake yi miki wani abu yana sane ko bai sani ba to ki samu wani lokaci da yake cikin nutsuwa ko yake cikin nishadi ki nuna masa cikin tausasa harshe misali “wane kayi min kaza nasan in Allah ya yarda zai dau kuskuren shi kuma za ki kuma shiga zuciyar shi. 


2. Yawan Mita

Duk macen da take da yawan mita in anyi abu baya wuce wa to za ta dinga sanewa maigidanta kuma bata fiya daraja a wajensa ba. 


3. Fushi 

Duk mace mai yawan fushi idan sun dan samu sabani da maigida mafi yawanci da namiji idan kuka sami dan sabani in ya fita ya manta to ke ki ringa yin fushi ko ya dawo ki daura sabon fushi yana sa mace ta fita daga zuciyar namiji yana da kyau yar uwa ta rika kai zuciyarta nesa


4. Rashin Iya Girki 

Girki-wani ginshiki ne na sinadarin zaman aure rashin iya shi yana kawo matsala tsakanin maigida da uwar gida in dai har baya samun jin dadin abincin da uwargida ke yi har yaji abincin da zai ci na waje yafi na gida dadi matsala ta faru domin yana ragewa uwargida daraja iya girki yana sa maigida yaso uwargidansa.


Idan maigida ya wadata iyalinsa da abinci to yakamata uwargida ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta iya salo-salo na tasarinfin abinci. Kuma hakikanin gaskiya tattalin arziki yana tasiri wajan wadata komai to amma bahaushe yace da ruwan ciki wai ake jan na rijiya don haka yar uwa idan har za ki kula da abin da maigida zai ci ba wai kullum abu daya ba ki kasance ko wane fanni na girki kin kware akwai marubuta da sukayi kokarin rubuta littafan koyon girke-girke yana da kyau uwargida ta nazarci irin wadannan littafan don koyon salo-salo na girki.


Duk lokacin da maigida ya dawo zai tarar kin gama komai na abinci sannan akwai wani sirri na girki da yawanci maigidanta suka fi so shine duk sanda yar uwa ta kawowa maigida abinci ta zauna a gabanshi yana ci kina yi mishi hira mai dadi rashin haka yana saka mace ta fita daga zuciyar namiji.


5. Rashin Baiwa Maigida Hakkinsa 

Rashin biyawa maigida bukatarshi wajen kwanciya illah ce babba da take kawo tabarbarewar aure duk sanda maidiga zai neme ki za ki yi raki ko ki tsaya jin kunyarshi yana sa mace ta fita daga zuciyar maigida amma idan har mace za ta zama mai jure bukatar mijinta tare da rashin gajiyawa ko tana so ko bata so karta yadda ya gane ko da tana cikin halin (period) ne akwai hanyoyi da dama da zata gamsar da shi.


Wannan sune abubuwa 5 dake jawo mace ta fita daga zuciyar mijinta duk irin tsananin son dake tsakanin su, da fatan amarya da uwargida za'a kiyaye da wadannan abubuwan kuma a gyara. Allah ya dawwamar da zaman lafiya a gidan ma'aurata amin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post