Yadda Ƙarancin wutar lantarki ya jefa al'umma cikin wahala - Android Pols



Al'umma na kuka akan ƙarancin wutar lantarki da ake samu, musamman a lokacin ibadar Azumin watan Ramadan, da al'ummar musulmi ke bukatar wutar, domin amfanin yau da kullum, kama daga samun ruwan sha, ruwa mai sanyi don buda baki, da sauransu. 


Yayin da al'umma ke wannan kuka, kamfanin dake rarraba hasken wutar lantarki a Jihohin Kano, Katsina da Jigawa (KEDCO), yace an samu ƙarancin wutar lantarkin ne saboda tattalin wutar da ake sakamakon ƙarancinta da suke fuskanta, amma tuni Injiniyoyin su suka dukufa don kawo karshen matsalar. 


Wasu da suka aike mana da saƙonni, sun ce sam basu gamsu da uzurin KEDCO ba, suna mai bayyana cewa kamar akwai adawa tsakanin kamfanin da kuma watan Ramadan, domin duk shekara hakan ce ke kasancewa. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post