Yadda Ake Karya Sihiri Da Lalata Sharrin Aljanu A Musulunci - Android Pols



A yanzu ina so ne in kawo muku yadda za ka lalata SIHIRIN da aka yi maka ko aka yi wa wani ko kuma korar Aljanun da suka damu mutane insha Allahu.


Amma yana da kyau in fara yin bayanin Alamomin da in ka ji su a tare da kai za ka gane an yi maka sihiri ko kuma an yi wa wani, sannan in kawo maka yadda za ka warware shi ta hanyar Ayoyin Alqur'ani da addu'o'in Manzoni Allah (SAW).

Yadda za ka gane kana da Aljanu ko kuma an yi maka Sihiri. 


Ana gane mai Aljanu ne ko wanda aka yiwa

sihiri ta hanyoyi guda uku:

1) Alamomin boye.

2) Alamomin sirri.

3) Alamomin zahiri.


1. Alamomin boye sune alamomin da shi maral lafiyar ne kawai ya ke iya ji ko ganin su a tare da shi.

Kamar

*Yawan mafarki mai abin tsoro.

*Yawan ciwon kai dab da magriba.

*Jin abu nai ma yawo a jiki kamar kiyashi.

*Haka kawai gaban mutum ya dinga faduwa.

*yawan mafarkin saduwa.

*Rashin son yin aure.

*Bacin rai mara dalili.

*Yawan tunane_tunane marasa amfani.

*Gane-ganen abubuwan tsoro kamar karnuka,

macizai, kuraye da dai sauran su.

*Jin kasala lokacin da za ka yi sallah.

*Jin ciwon kai lokacin da ake karanta

Alqur‘ani.

*Rashin fahimtar karatu ko kuma saurin

zubewar sa, musamman ma na addini.

*yawan jin an kira sunan ka kuma ka waiwaya ba ka ga kowa ba.

*yawan jin kamar an caka ma ka kibiya ko

allura a jiki.

*za ka kwanta barci da wuri amma ya ki

daukar ka sai dab da asuba.

*Yawan batan kudi ko kayan amfani.

*Yawan fada ko gaba da mutane.

Da dai sauran alamomi.


Ya a ke gane mai Aljanu? ko wanda aka jefe

shi da Sihiri(kashi na biyu)

Ana gane mai Aljanu ne ta hanyoyi guda uku


Kamar yadda mu ka fada tun a farko

1) Alamomin boye

2) Alamomin sirri

3) Alamomin zahiri

Mun yi bayanin alamomin boye, yanzu ga

alamomin sirri.

Alamomin sirri alamomi ne wadanda se

wanda ke tare da mara lafiyar ko da yaushe shi ne zai dinga ganin su ko fuskantar su.

* Mutum ya dinga magana a lokacin da ya ke

bacci.

* Nauyin Bacci mara misali.

* Dadewa a bandaki alhali ba abin da mutum ya ke yi.

* saurin fushi.

*Son zama a duhu.

*Son zama a waje mai kazanta.

*Zama da kazanta da rashin son yin wanka.

*Surutu barkatai.

*Rashin dariya ko murmushi sanda a ke abin

dariya.

*Rashin son yin sallah.

*Yawan harare-harare.

*Kura wa mutane ido.

*Yawan dariya ko murmushi ba dalili.

*Taurin kai.

*Rashin samari ga Budrwa.

Da dai alamomi da yawa.


YADDA AKE KARYA SIHIRI KO ‘KONA ALJANI


Wanda wadannan alamomi ko kuma mafiya

yawansu suka tabbata a tare da shi sai ya dinga yawan karanta wadannan ayoyi da addu'o'i Kuma ya dinga tofawa a ruwa yana sha yana shafe jikinsa.

( ﺍﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠّﻪِ ﺭَﺏِّ ﺍﻟْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ، ﺍﻟﺮَّﺣْﻤﻦِ ﺍﻟﺮَّﺣِﻴﻢِ، ﻣَﺎﻟِﻚِ

ﻳَﻮْﻡِ ﺍﻟﺪِّﻳﻦِ، ﺇِﻳَّﺎﻙَ ﻧَﻌْﺒُﺪُ ﻭﺇِﻳَّﺎﻙَ ﻧَﺴْﺘَﻌِﻴﻦُ، ﺍﻫﺪِﻧَﺎ

ﺍﻟﺼِّﺮَﺍﻁَ ﺍﻟﻤُﺴﺘَﻘِﻴﻢَ، ﺻِﺮَﺍﻁَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺃَﻧﻌَﻤﺖَ ﻋَﻠَﻴﻬِﻢْ ﻏَﻴﺮِ

ﺍﻟﻤَﻐﻀُﻮﺏِ ﻋَﻠَﻴﻬِﻢْ ﻭَﻻَ ﺍﻟﻀَّﺎﻟِّﻴﻦَ )

( ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﻣَﺎ ﺗَﺘْﻠُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦُ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﻠْﻚِ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ﻭَﻣَﺎ

ﻛَﻔَﺮَ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥُ ﻭَﻟَﻜِﻦَّ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ

ﺍﻟﺴِّﺤْﺮَ ﻭَﻣَﺎ ﺃُﻧﺰِﻝَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﻜَﻴْﻦِ ﺑِﺒَﺎﺑِﻞَ ﻫَﺎﺭُﻭﺕَ

ﻭَﻣَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎ ﻳُﻌَﻠِّﻤَﺎﻥِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﻘُﻮﻻ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻧَﺤْﻦُ

ﻓِﺘْﻨَﺔٌ ﻓَﻼ ﺗَﻜْﻔُﺮْ ﻓَﻴَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣِﻨْﻬُﻤَﺎ ﻣَﺎ ﻳُﻔَﺮِّﻗُﻮﻥَ ﺑِﻪِ ﺑَﻴْﻦَ

ﺍﻟْﻤَﺮْﺀِ ﻭَﺯَﻭْﺟِﻪِ ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢْ ﺑِﻀَﺎﺭِّﻳﻦَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺇِﻻ ﺑِﺈِﺫْﻥِ

ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻳَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﻳَﻀُﺮُّﻫُﻢْ ﻭَﻻ ﻳَﻨﻔَﻌُﻬُﻢْ ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﻋَﻠِﻤُﻮﺍ

ﻟَﻤَﻦْ ﺍﺷْﺘَﺮَﺍﻩُ ﻣَﺎ ﻟَﻪُ ﻓِﻰ ﺍﻵﺧِﺮَﺓِ ﻣِﻦْ ﺧَﻼﻕٍ ﻭَﻟَﺒِﺌْﺲَ ﻣَﺎ

ﺷَﺮَﻭْﺍ ﺑِﻪِ ﺃَﻧﻔُﺴَﻬُﻢْ ﻟَﻮْ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ ) ( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ –

102 )

( ﺀﺍﻣَﻦَ ﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝُ ﺑِﻤَﺎ ﺃُﻧﺰِﻝَ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻣِﻦْ ﺭَﺑِّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ

ﻛُﻞٌّ ﺀﺍﻣَﻦَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻣَﻼﺋِﻜَﺘِﻪِ ﻭَﻛُﺘُﺒِﻪِ ﻭَﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻻ ﻧُﻔَﺮِّﻕُ ﺑَﻴْﻦَ

ﺃَﺣَﺪٍ ﻣِﻦْ ﺭُﺳُﻠِﻪِ ﻭَﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺳَﻤِﻌْﻨَﺎ ﻭَﺃَﻃَﻌْﻨَﺎ ﻏُﻔْﺮَﺍﻧَﻚَ ﺭَﺑَّﻨَﺎ

ﻭَﺇِﻟَﻴْﻚَ ﺍﻟْﻤَﺼِﻴﺮُ ﻻ ﻳُﻜَﻠِّﻒُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻧَﻔْﺴًﺎ ﺇِﻻ ﻭُﺳْﻌَﻬَﺎ ﻟَﻬَﺎ ﻣَﺎ

ﻛَﺴَﺒَﺖْ ﻭَﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻣَﺎ ﺍﻛْﺘَﺴَﺒَﺖْ ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﻻ ﺗُﺆَﺍﺧِﺬْﻧَﺎ ﺇِﻥْ ﻧَﺴِﻴﻨَﺎ

ﺃَﻭْ ﺃَﺧْﻄَﺄْﻧَﺎ ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﻭَﻻ ﺗَﺤْﻤِﻞْ ﻋَﻠَﻴْﻨَﺎ ﺇِﺻْﺮًﺍ ﻛَﻤَﺎ ﺣَﻤَﻠْﺘَﻪُ

ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻠِﻨَﺎ ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﻭَﻻ ﺗُﺤَﻤِّﻠْﻨَﺎ ﻣَﺎ ﻻ ﻃَﺎﻗَﺔَ ﻟَﻨَﺎ

ﺑِﻪِ ﻭَﺍﻋْﻒُ ﻋَﻨَّﺎ ﻭَﺍﻏْﻔِﺮْ ﻟَﻨَﺎ ﻭَﺍﺭْﺣَﻤْﻨَﺎ ﺃَﻧْﺖَ ﻣَﻮْﻻﻧَﺎ

ﻓَﺎﻧﺼُﺮْﻧَﺎ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻘَﻮْﻡِ ﺍﻟْﻜَﺎﻓِﺮِﻳﻦَ ) ( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ 285 – ،

286 )

(ﻓَﻠَﻤَّﺎ ﺃَﻟْﻘَﻮْﺍ ﻗَﺎﻝَ ﻣُﻮﺳَﻰ ﻣَﺎ ﺟِﺌْﺘُﻢْ ﺑِﻪِ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ

ﺳَﻴُﺒْﻄِﻠُﻪُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻻَ ﻳُﺼْﻠِﺢُ ﻋَﻤَﻞَ ﺍﻟْﻤُﻔْﺴِﺪﻳﻦَ، ﻭَﻳُﺤِﻖُّ

ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﺤَﻖَّ ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺗِﻪِ ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺮِﻩَ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣُﻮﻥَ ) ( ﻳﻮﻧﺲ )

( ﻭَﺃَﻟْﻖِ ﻣَﺎ ﻓِﻲ ﻳَﻤِﻴﻨِﻚَ ﺗَﻠْﻘَﻒْ ﻣَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ

ﻛَﻴْﺪُ ﺳَﺎﺣِﺮٍ ﻭَﻻَ ﻳُﻔْﻠِﺢُ ﺍﻟﺴَّﺎﺣِﺮُ ﺣَﻴْﺚُ ﺃَﺗَﻰ ﻓَﺄُﻟْﻘِﻲَ

ﺍﻟﺴَّﺤَﺮَﺓُ ﺳُﺠَّﺪًﺍ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺁﻣَﻨَّﺎ ﺑِﺮَﺏِّ ﻫَﺎﺭُﻭﻥَ ﻭَﻣُﻮﺳَﻰ )

( 70 ﻃﻪ )

( ﺃَﻓَﺤَﺴِﺒْﺘُﻢْ ﺃَﻧَّﻤَﺎ ﺧَﻠَﻘْﻨَﺎﻛُﻢْ ﻋَﺒَﺜﺎً ﻭَﺃَﻧَّﻜُﻢْ ﺇِﻟَﻴْﻨَﺎ ﻟَﺎ

ﺗُﺮْﺟَﻌُﻮﻥَ، ﻓَﺘَﻌَﺎﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﻤَﻠِﻚُ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﻫُﻮَ ﺭَﺏُّ

ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻜَﺮِﻳﻢِ، ﻭَﻣَﻦ ﻳَﺪْﻉُ ﻣَﻊَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻟَﻬﺎً ﺁﺧَﺮَ ﻟَﺎ ﺑُﺮْﻫَﺎﻥَ

ﻟَﻪُ ﺑِﻪِ ﻓَﺈِﻧَّﻤَﺎ ﺣِﺴَﺎﺑُﻪُ ﻋِﻨﺪَ ﺭَﺑِّﻪِ ﺇِﻧَّﻪُ ﻟَﺎ ﻳُﻔْﻠِﺢُ ﺍﻟْﻜَﺎﻓِﺮُﻭﻥَ،

ﻭَﻗُﻞ ﺭَﺏِّ ﺍﻏْﻔِﺮْ ﻭَﺍﺭْﺣَﻢْ ﻭَﺃَﻧﺖَ ﺧَﻴْﺮُ ﺍﻟﺮَّﺍﺣِﻤِﻴﻦَ )

( ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ 115: 118 )

( ﻳَﺎ ﻣَﻌْﺸَﺮَ ﺍﻟْﺠِﻦِّ ﻭَﺍﻟْﺈِﻧﺲِ ﺇِﻥِ ﺍﺳْﺘَﻄَﻌْﺘُﻢْ ﺃَﻥ ﺗَﻨﻔُﺬُﻭﺍ

ﻣِﻦْ ﺃَﻗْﻄَﺎﺭِ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻓَﺎﻧﻔُﺬُﻭﺍ ﻟَﺎ ﺗَﻨﻔُﺬُﻭﻥَ ﺇِﻟَّﺎ

ﺑِﺴُﻠْﻄَﺎﻥٍ، ﻓَﺒِﺄَﻱِّ ﺁﻟَﺎﺀ ﺭَﺑِّﻜُﻤَﺎ ﺗُﻜَﺬِّﺑَﺎﻥِ، ﻳُﺮْﺳَﻞُ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻤَﺎ

ﺷُﻮَﺍﻅٌ ﻣِّﻦ ﻧَّﺎﺭٍ ﻭَﻧُﺤَﺎﺱٌ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻨﺘَﺼِﺮَﺍﻥِ، ﻓَﺒِﺄَﻱِّ ﺁﻟَﺎﺀ

ﺭَﺑِّﻜُﻤَﺎ ﺗُﻜَﺬِّﺑَﺎﻥِ ) ( ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ 33: 36 )

( ﻗُﻞْ ﺃُﻭﺣِﻲ ﺇِﻟَﻲّ ﺃَﻧَّﻪُ ﺍﺳْﺘَﻤَﻊَ ﻧَﻔَﺮٌ ﻣِﻦْ ﺍﻟْﺠِﻦِّ ﻓَﻘَﺎﻟُﻮﺍ ﺇِﻧَّﺎ

ﺳَﻤِﻌْﻨَﺎ ﻗُﺮْﺁﻧًﺎ ﻋَﺠَﺒًﺎ، ﻳَﻬْﺪِﻱ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﺮُّﺷْﺪِ ﻓﺌﺎﻣَﻨَّﺎ ﺑِﻪِ ﻭَﻟَﻦْ

ﻧُﺸْﺮِﻙَ ﺑِﺮَﺑِّﻨَﺎ ﺃَﺣَﺪًﺍ، ﻭَﺃَﻧَّﻪُ ﺗَﻌَﺎﻟَﻰ ﺟَﺪُّ ﺭَﺑِّﻨَﺎ ﻣَﺎ ﺍﺗَّﺨَﺬَ

ﺻَﺎﺣِﺒَﺔً ﻭَﻻ ﻭَﻟَﺪًﺍ، ﻭَﺃَﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻳَﻘُﻮﻝُ ﺳَﻔِﻴﻬُﻨَﺎ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ

ﺷَﻄَﻄًﺎ، ﻭَﺃَﻧَّﺎ ﻇَﻨَﻨَّﺎ ﺃَﻥْ ﻟَﻦْ ﺗَﻘُﻮﻝَ ﺍﻹﻧﺲ ﻭَﺍﻟْﺠِﻦُّ ﻋَﻠَﻰ

ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻛَﺬِﺑًﺎ، ﻭَﺃَﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﺭِﺟَﺎﻝٌ ﻣِﻦْ ﺍﻹﻧﺲ ﻳَﻌُﻮﺫُﻭﻥَ

ﺑِﺮِﺟَﺎﻝٍ ﻣِﻦْ ﺍﻟْﺠِﻦِّ ﻓَﺰَﺍﺩُﻭﻫُﻢْ ﺭَﻫَﻘًﺎ، ﻭَﺃَﻧَّﻬُﻢْ ﻇَﻨُّﻮﺍ ﻛَﻤَﺎ

ﻇَﻨَﻨﺘُﻢْ ﺃَﻥْ ﻟَﻦْ ﻳَﺒْﻌَﺚَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪًﺍ، ﻭَﺃَﻧَّﺎ ﻟَﻤَﺴْﻨَﺎ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ

ﻓَﻮَﺟَﺪْﻧَﺎﻫَﺎ ﻣُﻠِﺌَﺖْ ﺣَﺮَﺳًﺎ ﺷَﺪِﻳﺪًﺍ ﻭَﺷُﻬُﺒًﺎ، ﻭَﺃَﻧَّﺎ ﻛُﻨَّﺎ

ﻧَﻘْﻌُﺪُ ﻣِﻨْﻬَﺎ ﻣَﻘَﺎﻋِﺪَ ﻟِﻠﺴَّﻤْﻊِ ﻓَﻤَﻦْ ﻳَﺴْﺘَﻤِﻊْ ﺍﻷﻥَ ﻳَﺠِﺪْ ﻟَﻪُ

ﺷِﻬَﺎﺑًﺎ ﺭَﺻَﺪًﺍ ) ( ﺍﻟﺠﻦ – 1 ، 9 )

( ﻗُﻞْ ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟْﻜَﺎﻓِﺮُﻭﻥَ، ﻻ ﺃَﻋْﺒُﺪُ ﻣَﺎ ﺗَﻌْﺒُﺪُﻭﻥَ، ﻭَﻻ ﺃَﻧْﺘُﻢْ

ﻋَﺎﺑِﺪُﻭﻥَ ﻣَﺎ ﺃَﻋْﺒُﺪُ، ﻭَﻻ ﺃَﻧَﺎ ﻋَﺎﺑِﺪٌ ﻣَﺎ ﻋَﺒَﺪﺗُّﻢْ، ﻭَﻻ ﺃَﻧْﺘُﻢْ

ﻋَﺎﺑِﺪُﻭﻥَ ﻣَﺎ ﺃَﻋْﺒُﺪُ، ﻟَﻜُﻢْ ﺩِﻳﻨُﻜُﻢْ ﻭَﻟِﻯﻲ ﺩِﻳﻦِ )

( ﺍﻟﻜﺎﻓﺮﻭﻥ )

( ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ، ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟﺼَّﻤَﺪُ، ﻟَﻢْ ﻳَﻠِﺪْ ﻭَﻟَﻢْ ﻳُﻮﻟَﺪْ،

ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﻟَﻪُ ﻛُﻔُﻮًﺍ ﺃَﺣَﺪٌ ) ( ﺍﻹﺧﻼﺹ )

( ﻗُﻞْ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﺮَﺏِّ ﺍﻟْﻔَﻠَﻖِ، ﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺧَﻠَﻖَ، ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ

ﻏَﺎﺳِﻖٍ ﺇِﺫَﺍ ﻭَﻗَﺐَ، ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﺍﻟﻨَّﻔَّﺎﺛَﺎﺕِ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻌُﻘَﺪِ، ﻭَﻣِﻦْ

ﺷَﺮِّ ﺣَﺎﺳِﺪٍ ﺇِﺫَﺍ ﺣَﺴَﺪَ ) ( ﺍﻟﻔﻠﻖ )

( ﻗُﻞْ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﺮَﺏِّ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ، ﻣَﻠِﻚِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ، ﺇِﻟَﻪِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ، ﻣِﻦْ

ﺷَﺮِّ ﺍﻟْﻮَﺳْﻮَﺍﺱِ ﺍﻟْﺨَﻨَّﺎﺱِ، ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳُﻮَﺳْﻮِﺱُ ﻓِﻲ ﺻُﺪُﻭﺭِ

ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ، ﻣِﻦْ ﺍﻟْﺠِﻨَّﺔِ ﻭَﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ) ( ﺍﻟﻨﺎﺱ

ﻫﻮ ۞ ﺍﻟﻠﻪ ۞ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ۞ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ۞ ﺍﻟﻤﻠﻚ ۞ ﺍﻟﻘﺪﻭﺱ

۞ ﺍﻟﺴﻼﻡ ۞ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ۞ ﺍﻟﻤﻬﻴﻤﻦ ۞ ﺍﻟﻌﺰﻳﺰ ۞ ﺍﻟﺠﺒﺎﺭ

۞ ﺍﻟﻤﺘﻜﺒﺮ ۞ ﺍﻟﺨﺎﻟﻖ ۞ ﺍﻟﺒﺎﺭﺉ ۞ ﺍﻟﻤﺼﻮﺭ ۞ ﺍﻟﻐﻔﺎﺭ

۞ ﺍﻟﻘﻬﺎﺭ ۞ ﺍﻟﻮﻫﺎﺏ ۞ ﺍﻟﺮﺯﺍﻕ ۞ ﺍﻟﻔﺘﺎﺡ ۞ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ ۞

ﺍﻟﻘﺎﺑﺾ ۞ ﺍﻟﺒﺎﺳﻂ ۞ ﺍﻟﺨﺎﻓﺾ ۞ ﺍﻟﺮﺍﻓﻊ ۞ ﺍﻟﻤﻌﺰ ۞

ﺍﻟﻤﺬﻝ ۞ ﺍﻟﺴﻤﻴﻊ ۞ ﺍﻟﺒﺼﻴﺮ ۞ ﺍﻟﺤﻜﻢ ۞ ﺍﻟﻌﺪﻝ

ﺍﻟﻠﻄﻴﻒ ۞ ﺍﻟﺨﺒﻴﺮ ۞ ﺍﻟﺤﻠﻴﻢ ۞ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ۞ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ ۞

ﺍﻟﺸﻜﻮﺭ ۞ ﺍﻟﻌﻠﻲ ۞ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ ۞ ﺍﻟﺤﻔﻴﻆ ۞ ﺍﻟﻤﻘﻴﺖ ۞

ﺍﻟﺤﺴﻴﺐ ۞ ﺍﻟﺠﻠﻴﻞ ۞ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ ۞ ﺍﻟﺮﻗﻴﺐ ۞ ﺍﻟﻤﺠﻴﺐ

۞ ﺍﻟﻮﺍﺳﻊ ۞ ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ ۞ ﺍﻟﻮﺩﻭﺩ ۞ ﺍﻟﻤﺠﻴﺪ ۞ ﺍﻟﺒﺎﻋﺚ

۞ ﺍﻟﺸﻬﻴﺪ ۞ ﺍﻟﺤﻖ ۞ ﺍﻟﻮﻛﻴﻞ ۞ ﺍﻟﻘﻮﻱ ۞ ﺍﻟﻤﺘﻴﻦ ۞

ﺍﻟﻮﻟﻲ ۞ ﺍﻟﺤﻤﻴﺪ ۞ ﺍﻟﻤﺤﺼﻲ ۞ ﺍﻟﻤﺒﺪﺉ ۞ ﺍﻟﻤﻌﻴﺪ ۞

ﺍﻟﻤﺤﻴﻲ ۞ ﺍﻟﻤﻤﻴﺖ ۞ ﺍﻟﺤﻲ ۞ ﺍﻟﻘﻴﻮﻡ ۞ ﺍﻟﻮﺍﺟﺪ ۞

ﺍﻟﻤﺎﺟﺪ ۞ ﺍﻟﻮﺍﺣﺪ ۞ ﺍﻷﺣﺪ ۞ ﺍﻟﺼﻤﺪ ۞ ﺍﻟﻘﺎﺩﺭ ۞

ﺍﻟﻤﻘﺘﺪﺭ ۞ ﺍﻟﻤﻘﺪﻡ ۞ ﺍﻟﻤﺆﺧﺮ ۞ ﺍﻷﻭﻝ ۞ ﺍﻵﺧﺮ ۞

ﺍﻟﻈﺎﻫﺮ ۞ ﺍﻟﺒﺎﻃﻦ ۞ ﺍﻟﻮﺍﻟﻲ ﺍﻟﻤﺘﻌﺎﻟﻲ ۞ ﺍﻟﺒﺮ ۞

ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ۞ ﺍﻟﻤﻨﺘﻘﻢ ۞ ﺍﻟﻌﻔﻮ ۞ ﺍﻟﺮﺀﻭﻑ ۞ ﻣﺎﻟﻚ ۞

ﺍﻟﻤﻠﻚ ۞ ﺫﻭ ۞ ﺍﻟﺠﻼﻝ ۞ ﻭﺍﻹﻛﺮﺍﻡ ۞ ﺍﻟﻤﻘﺴﻂ ۞

ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ۞ ﺍﻟﻐﻨﻲ ۞ ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ۞ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ۞ ﺍﻟﻀﺎﺭ ۞

ﺍﻟﻨﺎﻓﻊ ۞ ﺍﻟﻨﻮﺭ ۞ ﺍﻟﻬﺎﺩﻱ ۞ ﺍﻟﺒﺪﻳﻊ ۞ ﺍﻟﺒﺎﻗﻲ ۞

ﺍﻟﻮﺍﺭﺙ ۞ ﺍﻟﺮﺷﻴﺪ ۞ ﺍﻟﺼﺒﻮﺭ

Insha Allahu Sihiri zai karye kuma Aljanu za su bar jikin mutum.

Idan mutum ya gwada bai samu lafiya ba to mai yiwuwane Larurar ta yi karfin da sai an yi masa Rukiyya ko kuma an ba shi Magungunan karya Sihiri da na kona Aljanu.


MAGUNGUNAN DA SUKE MAGANIN ALJANI

KOWANNE IRE NE KO DA KO NA SIHIRI NE

INSHA ALLAHU.


1.HILTIT:- wannan wani maganine da ake

samoshi a jikin wata bishiya mai suna(Anjudan) kamshinsa yana shake aljani koma ya kasheshi, saboda haka ake shan kadan ko ayi turare dashi.


2.AKIRUKARHA:- wani ganye ne da yake yado a bayan kasa kuma yana da fure yallow, yana azabtar da aljani musamman ma bakin aljani, kuma ayana maganin farafdiya da rashin haihuwa da sauransu.


3.AMBAR:- Idan an hadashi da man zaitun da habbatu sauda anashafawa yana hallaka aljani,k uma yana kara soyayya tsakanin muji da mata.


4.SI'ITIR:- Yana fitar da sihiri, yana maganin Yanar ido idan anyi kwalli dashi.


5: ‘KUS‘DUL HINDI:- Wannan maganin yana

hallaka aljani, kuma yana fitar da haila idan ta tsaya, idan kuma ana yawaita amfani dashi yana kashe aljani.


6.KIRIFAT: Wani 6awo ne mai dandano mai zaki mai kuma dadin kamshi, Idan anhadashi da yan son anayin shayi dashi yana maganin sihiri, kuma maganin hawan jini, asthma, wasu was, ciwon saifa da sauransu.


7.YANSUN: wanan magani ana hada shi da habbatusauda da zuma domin fitar da aljani.


8:SAFARJAL:- Yana maganin wasu wasi,k uma yana maganin shafar aljani da shan Inna.


9.ISMUDI: Tozalin Annabi (s a w) yana maganin Idon da aljani ya rufe, da kuma ciwon kai, da Yanar ido,


10. SHAJARATU MARYAM:- Tana fitar da aljani daga cikin jijiya kuma tana fitar da sihiri da aka sha.


11.ALBABUNAJ:- Yana bin aljani duk inda yake a jikin dan adam ya fitartar dashi cikin sauki.


12. SABULUN MUGTASAL :- Yana maganin

kurajen jiki da na fuska. yana kara karfin maza.

Yana tilastawa Aljani barin jkin mutum. Yana toshe hanyoyin da Aljani ke bi domin shiga jikin Dan Adam kuma yana maganin amosanin kai. Yana maganin kaikayin jiki.


YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN DA KE KONA AL-JANI DA KASHE SHI.


1- A samu Kaikayi-koma-kan-mashekiya, tazargade, jema, hiltit da nono. Sai a hadasu waje daya a dafa. Idan an dafa sai a raba biyu, rabi a dinga zubawa a nono ana sha, rabin kuma a dinga yin wanka da shi. Yana maganin farfadiya da Jinnul katfa masu make mutane, da ciwon barin jiki wanda Aljanu su ka haifar.


2- Kwankawatsen mahauta, tsamiyar makiyaya, da bakin bunu. Sai a hada su waje daya a dinga hayaki da shi a jiki kullum, don maganin bakaken Aljanu. Yana kuma hana Aljanu shiga gida da ra6ar wajen da aka turara saidai yana karya magunguna marasa karfi da suke kusa da shi. 

.

3- Ma'ul wardi, ma'ul khal da kuma alkahauli, sai a hada su waje daya, a hada da ruwa kadan a dinga shafe jiki da shi. Yana toshe hanyoyin da Aljanu suke shiga jikin mutane yana kuma fitar da su cikin gaggawa.

.

4- Tsakin kuka, bintil sudan, sassaken dogon yaro da kuma furen tumfafiya. Sai a hada su waje daya a daka, a jika a cikin turaren, a dinga shafe jiki da shi. Sariqul jinni, rariyar hannu da namijin dare, duk wannan hadin yana maganinsu.

.

5- Ma'ul wardi, ma'ul khal, hiltit da zuma. A jada su waje daya, a dinga zubawa a ruwa, ana sha, kullum sau daya. Idan Aljanu suka rikewa mutum baki ya kasa magana bakin zai bude. Yana maganin ciwin ciki da kirji da mara, wadanda Aljanu suka haifar.

.

6- Jan kajiji, bakin kaji, habbatus saudaaa, habbatur rashad, farar wuta da kuma tafarnuwa. A hada su a daka. Sai a raba biyu, rabi a kwa6a da man kadanya a dinga shafe jiki da shi, rabin kuma a dinga yin hayaki da shi. Yana maganin ciwon daji da kansar mama da fatar da Aljanu suka 6ata. Yana hana Aljanu shiga jikin mutum yana kuma korarsu daga gida.

.

7- Nonon giwa, jan miski, kustul hidiy, farar wuta, man gelo, da ma'ul khal. A hada su waje daya, sai a dinga shaka, kullum sau uku. Yana fitar da Aljani daga jikin mutum nan take. Yana maganin ciwon kai da ciwon kirji wadanda Aljanu su ka haifar yana kuma saurin kona Aljani da kashe shi.

.

8- Turaren Ambar, turaren za'afaran, jan miski, bakin miski, da kuma man juda. A hada su waje daya, a dinga shafe jiki kullum idan za a kwanta barci da adaddare. Yana maganin namijin dare da mugwayen mafarkai da figita da rashin barci wanda Aljanu su ka haifar.

.

9- Man juda, habbatus saudaa, man zaitun, man gelo, zuma da man tafarnuwa, a hada su waje daya, a dinga shan cokali daya kullum. Yana saurin kashe Aljani har lahira, yana magani cututtuka da Aljanu su ka saka a jikin mutum.

.

10- Bakin hayaki, bakin bunu, da kuma baduhun shuri. A hada su waje daya, a dinga hayaki kullum sau biyu amma hayakin daki da gida ake turarawa. Yana korar Aljanu da suke zaune a gidan mutane ko wajen aiki sannan yana fitar da Aljani daga jikin mutum.

.

11- Turar ruwa, gashin jima, Fusuhul jinni, da hiltit. A hada su waje daya, a dinga hayaki kullum sau daya. Wannan hadin yana karya sihiri yana maganin yawan faduwar gaba da 6acin rai mara dalili da ciwon kan lokacin magriba da jin haushin mutane ba dalili.

.

12- Buruku, ganyen raidore, duman rafi da kaikayi-koma-kan-mashekiya. A tafasa a dinga sha da wanka. Maganin Kowace irin lalura ta Aljanu wacce ta shafi cikin jiki.

.

13- Sassaken gawo, kaikayi koma kan mashekiya, sassaken katsari. A dafa, sha da wanka. Yana magani sammu da maita da baki da kambun ido.

.

14- Ganyen sarkakiya, ganyen sidr da garin sabara. A dafa su tare, a dinga sha. Maganin kowace cuta ta jinnu wacce take cikin jiki.

.

15- Sabulun zaitun, sabulun habba, tafarnuwa, ganyen magarya da jan miski. A hada sabulan waje daya, sai a kir6a tafarnuwa a zuba ma ta ruwa a matse, a zuba acikin sabulun da turaren a dinga wanka da shi. Yana gyara fata wacce Aljanu su ka 6ata sannan yana toshe hanyoyin da Aljani ke bi domin shiga jikin mutum. 

.

16- Bakin magani, sanamakiy, garin sabara, da kuma garin rawaya kadan. Sai a tafasa da lemon tsami ko tsamiya, idan ya huce a dinga sha. Maganin kowacce laurara wacce Aljani ya saka a cikin jiki.

.

17- Ganyen kaba da kuma jema. A jika su a sabuwar tukunyar kasa a dinga sha. Yana maganin fitsarin kwance na manya da yara, yana maganin maita da Aljanu mazauna cikin gida.

.

18- Shuhurul jinni, du'a'ul jannnah da muhriqul jinni. A daka muhriqul jinnin a jika shi acikin turarukan, a dinga shafe jiki da shi. Yana maganin Aljani mai taurin naci, yana hana shi shiga jikin mutum.

.

19- Azfarul jinni da shajaratu Maryam. A jika su tare a dinga sha. Magani ciwon ciki, matsalar nakuda, kwanciyar ciki da yawan 6ari. Tana bin Aljani duk inda ya shiga ajikin mutum ta fitar da shi cikin sauki da yaddar Allah.

.

20- Kanwa, gishiri da albasa. A hada su waje daya, a jika a cikin kwarya, a dinga sha. Yana magani cutar Aljani tare da karya sihiri cikin sauki.

.

21- Farin hayaki, tazargade, ganyen kaba, da habbatussauda. A hada a dinga hayaki da su. Maganin namijin dare, maita da sauran cututtukan Aljanu.

.

22- Ganyen na'ana'a, raihan, jema, zuma da kuma garin bakin bunu. A dinga dafawa ana yin shayi da su. Yana maganin rashin gane karatu, shirita da fitar da sihiri daga jikin mutum. 

.

23- Kamfani, bintil sudan, jan miski, shuhurul jinni, ma'ul jinni. A hade su waje daya, a dinga shafe jiki da shi. Yana hana Aljani shiga shiga mutum yana kuma fitar da wanda yake ciki.

.

24- Kafoor mash'hoor, gadali, man kadanya a hada waje daya a dinga shafawa a hannu da kafafuwa. Yana toshe hanyoyin da Aljani yake bi domin shiga jikin mutum.

.

25- Ganyen aduwa, ganyen magarya, ganyen dinya da ganyen sarkakiya. A dinga dafawa, sha da wanka. Maganin kowace irin cutar Aljani ta cikin jiki.

.

26- Garin sanya, hannu, fasakwari, sassaken 6aure, bakin magani. A dafa a dinga sha amma sanyar kadan ake zuba ta. Maganin fitsarin kwance, firgita da mugwayen mafarkai.

.

27- `Ya`yan zurman, bakin algaru, jan algaru ganyen tumfafiya. A hada waje daya a dinga turarawa acikin gida da cikin dakuna. Yana korar Aljanu daga gida kuma yana hana Aljanu shiga gidan.

.

28- Jan miski. `ya`yan zurman, man juda, Kafoor mash'shoor. A hada su waje daya a dinga shafawa a ga6o6in jiki guda talatin. Yana toshewa Aljani hanyar shiga jikin dan'Adam.


Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin rukiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700.


AMMA A KULA

Ya kamata duk wanda zai yi amfani da wadannan magunguna to ka tuntu6i masani akan fannin magani domin yay maka bayanin gwargwadon yadda za kay amfani da kowanne sannan a ware ma ka maganin da mace mai ciki ba ta sha da wanda ba a baiwa kananan yara da dai sauran dokoki da su ka danganci Magani. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post