Yadda Aka Yi Amfani Da Giya Wajen Siyan Kuri'u A Jihar Benue - Android Pols


Ƙungiyar rajin kawo ci gaba ta YIAGA, ta ce bayanan da ta tattara sun nuna yadda ƴan siyasa suka rinƙa amfani da abubuwa daban-daban wajen sayen ƙuri’a a zaɓen gwamnonin Najeriya.


Jami’in ƙungiyar, Paul James, ya ce sun samu rahotannin sayen ƙuri’u a jihohi da dama, ciki har da irin su Bauchi da Benue.


Ya ce a Makurdi, babban birnin jihar Benue, an rinƙa saya wa mutane barasa domin su kaɗa ma wasu 'yan takara ƙuri’a.


Haka nan a cewarsa an yi amfani da kuɗi sosai a lokacin zaɓen na gwamnoni wanda ya gudana a ranar Asabar.


A tattaunawar da ya yi da BBC a safiyar Lahadi, James ya ce babban abin takaicin shi ne yadda wakilan jam’iyyu suka rinƙa kaɗa wa mutane ƙuri’a bayan sun biya su kuɗi.


Ya kuma ƙara da cewa sun samu rahotannin wasu wuraren da aka ƙona ƙuri’u bayan kai farmaki a rumfunan zaɓe.


Wannan zaben dai ya sha bamban da zaben da aka yi na shugaban kasa a makonnin da suka gabata inda a wannan zaben na gwamnoni aka samu yawan siyan Kuri'u duk kuwa da kiraye-kirayen da mahukunta suke yi akan hakan. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post