Ko kunsan cewa za ku iya kawo karshen matsalar Ciwon ulcer da Ganyen gova (guava)?


Ulcer ciwo ne dake addabar al'umma a wannan zamanin wanda da wuya Kaje gida ka rasa wanda ba ya yi. Sai dai akwai hanyoyi da yawa da ake yin amfani dasu domin kawo karshen ciwon. 


Muna yawan kawo muku hanyoyin dai mutum zai yi amfani dashi wajen Magance wannan ciwo na gyambon ciki (Ulcer). Wanda yau ma gashi mun kawo muku wani da za ku yi amfani da ganyen gova don yin Magani. 


Maganin ciwon ulcer- Stomach ulcer- Wanda yake famada da ciwon ulcer.


(1) ulcer Mai riqe baya,

(2) ulcer Mai yawan sajin yunwa,

(3) ulcer Mai yawan da Ayi zawo

(4) ulcer Mai yawan sa saurin fishi

(5) ulcer Mai yawan sa kuke yin Amai wani lokacin ma aga jini-jini,

(6) ulcer.mai yawan yawan saka zafin kirji

(7) ulcer Mai yawan. Kumbura Ciki, dasa ciwon kai. 


Sai ku samu ganyen goba guda-10- a samu ruwa mai tsafta a wanke sosai, sai a samu tukunya Mai Kyau a zuba ruwa kamar liter daya one litter, a dora a wuta a zuba ganyan a cikin tukunyar tare da ruwan litter daya su dahu sosai har sai ruwan ya canza kala yakoma Kala ganyan sai a sauke a tace. 


A samu karamin kofi a dinga Shan kofi daya daya sau uku a rana. Wannan maganin yana kauda matsalar Ulcer da yardar Allah. Duk mai fama da ciwon ulcer ya jaraba zai ji Sauki. 


Haka mace mai ciki za ta iya shan maganin domin yana taimakawa gurin samun lafiyar yaro da saukin haihuwa.

 

Masu fama da matsalar ciwon sugar a samu ganyan goba da dan yawa a wanke a tafasa a tace ana yawan shansa yana saukar da sugar Idan an dage yana kashe ciwon sugar.


Masu fama da matsalar hawan jini

A samu ganyen gwaiba a wanke a dafa a samu Jan zoborodo a zuba kadan a ciki a tace a sha kamar sau hudu ko sau biyar amma ludayi ko karamin Kofi za'ayi amfani dashi. Wannan yana saukar da matsalar hawan jini. 


Mai famada matsalar ciwon rabin jiki wanda rabin jikinsa yashanye a samu yayan gwaiba wanda basu gama nuna ba a daka su a samu dabino shima a daka kowane ayi garin sai a samu nonon Rakumi a dibi cokali biyu na garin maganin kowane a hada a cikin nonon rakumi kamar karamin Kofi ake juyawa da bawa mara lafiyar yasha za'a sha da safe kafin ya karya da rana bayan an ci abinci da dare bayan anci abinci

  

Allah yabamu Lafiya. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post