HOTUNA: Yadda Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Farfasa Kwalaben Giya Miliyan Hudu - Android Pols


Sama da Kwalaben barasa miliyan hudu Dakarun Hukumar Hisbah suka Farfasa a Dutsen Kalibawa dake yankin karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano.


Lokacin da yake jawabi Babban Kwamandan Hisbah Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina, yace sun gabatar da aikin fasa barasar karo uku wannnan shine na karshe cikin jerin aikin da ya jagoranta a matsayisa na babban Kwamandan Hisbah.


Yace matukar aka bar kayan maye suna yawo a cikin Al'umma za a samu miyagun laifuka da sace-sace da sauransu.


Da yake jawabi Tun da fari Mataimakin Babban Kwamanda bangaren ayyukan yau da kullum Shehu Tasiu yace kayan da aka lalata sun Hadar da Giya da Sholisho da Shisha da kayan tsubbace-tsubbace, Yana mai cewa yanzu haka akwai motoci biyu na Tirela dake makare da kamru a ciki. 

 

Kwamishinan Addinai Kuma wakilin Gwamnan Kano Dr. Muhammad Nazeefi Bichi, yace wannnan aikine da ya kamata a cigaba da shi kamar yadda Gwamna Ganduje yayi domin kawar da kayan maye a Jihar Kano.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post