Amfanin Dabino Ga Lafiyar Dan Adam - Android Pols


Dabino Da Turanci (Date palm) (Phoenix dactilifeyra) itaciya ce dake fidda ya'ya kanana masu zaki da ake kira da yayan dabino, bishiyar dabino tana daga cikin jinsin bishiyoyi kamar bishiyoyin kwa-kwa mai ruwa da ta kwakwan manja. 


Kuma bishiyar dabino,bishiya ce mai ɗinbin tarihi Dabino yanada muhimmanci sosai a jikin dan Adam wato ana amfani dashi sosai don ƙara lafiya don kuwa yana ƙunshe da sinadaran gina jiki Yana Kuma kashe ƙwayoyin cuta kamar kansa da sauran su. Amfanin dabino baya ƙirguwa. 


Musulmi kanyi amfani da dabino a lokacin Azumi don buɗa baki don koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S A W). Don kuwa har cikin Alqur'ani mai girma Allah maɗaukakin sarki ya ambaci dabino sau da yawa don Kuma ƙarin bayani duba:


1. Suratul Bakara, Aya ta 226

2. An’am, Aya ta 99 da 141

3. Suratul Ra’ad, Aya ta 4

4. Suratul Nahli, Aya ta 11 da 67

5. Suratul Isra’i, Aya ta 91

6. Suratul Kahfi, Aya ta 32

7. Suratul Maryam, Aya ta 23 da 25

8. Suratul Daha, Aya ta 71

9. Suratul muminin, Aya ta 19

10. Suratul Shu’ara, Aya ta 148

11. Suratul Yasin, Aya ta 34

12. Suratul Ka’af, Aya ta 10

13. Suratul Kamar, Aya ta 7

14. Suratul Rahman, Aya ta 11 da 68

15. Suratul Ha’akkah, Aya ta 7

16. Suratul Abasa, Aya ta 29


Dabinon da ya bushe mai nauyin giram 30 na samar da:


81 kcal / 345KJ


Girma 1.0 na Abinci mai gina jiki


Giram 0.1 na ma su sa kiba


Girma 20.4 na abinci mai kara kuzari


Giram 20.4 na Suga


Giram 1.6 na nau'in narkar da abinci.


Giram 210 na sinadarin potashiyom


Bai wa jiki kariya


Dabino na da sinadarin da ke bai wa jiki kariya mai yawa.


Cikinsu akwai sinadaran polyphenols, da carotenoids, da lignans. Dukkansu sinadiran gina jiki ne da ke kare jikin ɗan Adam daga kamuwa daga cutuka masu tsanani.


Ƙara lafiyar ciki


Bincike kan abubuwan ci masu narkar da abinci na ci gaba da taka rawa mai mahimmanci ga lafiya, da taimakawa wajen tabbatar da lafiyar ciki, har ma da rage hadarin fama da cutuka masu tsayi.


Wani karamin bincike a 2015 ya gano cewa cin dabino zai iya rage kamuwa da ciwon kansa sakamakon sinadarin narkar da abinci na polyphenol, da amfanin da yake da shi wajen samar da sinadaren da ke taimakawa wajen kashe cutuka.


Ƙara lafiyar ƙashi


Dabino na da mahimmaci wajen kula da lafiyar ƙashi, saboda yadda yake dauke da sinadarin phosphorus, da potassium, da calcium da na magnesium.


Haka kuma dabino na da sinadarin karin lafiya na vitamin K da ke kara ƙarfin ƙashi.


Taimakawa wajen haihuwa cikin sauki


Cin dabino a makon karshe na mai ciki kafin haihuwa na taimakawa wajen rage tsayin naƙuda, sannan yana sa bakin mahaifa ya dinga budewa.


Haka kuma, ana kallon irin mahimmancin da suke da shi wajen takaita amfani aiki tsawon awanni.


Cikin sinadaran da dabino ya kunsa akwai oxytocin, wanda ke saukaka tsananin ciwon nakuda.


Ana Iya Amfani Da shi a Madadin Sukari


Ana shan ruwan dabinon bayan an jika shi a cikin ruwa.


Ruwan dabinon na da karancin sinadarin glycemic index (GI) da karancin sukarifiye da sauran na'ikan kayan zaki.


Maganin Gudawa 


Dabino na maganin cutar gudawa da dukanin wasu cututtuka masu nabasa da ciwo ko lalacewar ciki da ake kamuwa da su. 


Dabino na kara karfi da kuzari 


A dalilin irin sunadaran da ke ciki na Calcium, Sulphur, Iron da sauran su, Dabino na kara karfin kashi da kuma kwanjin mutum ya karu. Hakan ya sanya ake son fara cin dabino ga mai buda baki na sha ruwa bayan azumi domin kuwa yana kara karfi. Haka kuma ya sanya ake ba yaro da zarar an haife sa. 


Kara lafiyar kwakwalwa da kaifin basira 


Dabino ya kunshi sunadaran Vitamin B da kuma Choline, masu taka rawar gani wajen bunkasa lafiyar kwakwalwa da kaifin basira. Haka kuma wannan sunadarai suna taimako wajen yin riga-kafin kamuwa da cutar mantawa a yayin tsufa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post