Abubuwa 8 Kan Sabon Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf


A ranar litinin ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da Abba Kabir Yusuf(Abba Gida-Gida) a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.


Hakan yasa muka kawo muku jerin abubuwa 8 da ya dace ku sani game da shi:


 An haife shi ranar 5 ga watan January, 1963 a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.


Ya yi karatun Firamare a makarantar gwamnati da ke Sumaila Primary School sannan kuma ya yi karatun Sakandire a makarantar gwamnati ta Lautai a Gumel da ke jihar Jigawa.


Abba ya yi karatun difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Mubi sai kuma babbar difloma a kwalejin kimiya da fasaha ta Kaduna watau Kaduna Polytechnic.


Ya yi karatun digirinsa na biyu digiri a jam’iyyar Bayero ta Kano a fannin harkokin kasuwanci.


Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabi'u Musa Kwankwaso.


Abba gida-gida ya yi takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019 amma bai samu nasara ba.


Yana da mata biyu da ‘ya’ya da dama.


Ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano a ranar 20 ga watan Maris na 2023.


Wannan shine abu takwas da ya dace ku sani akan sabon gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf. Muna fatan Allah ya bashi ikon sauke nauyin dake kansa. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post