Yadda Al'Ameen G fresh ya gurfana a gaban Hukumar Hisbah - Android PolsYa gurfanane bisa zargin wasa da Sallah wanda sashin Kai Sumame na Hukumar Hisbah suka nemo shi kuma suka mikawa Sashin Da'awa na Hukumar Hisbah karkashin jagorancin Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah Ustaz Hussaini Ahmad Chediyyar Kuda bisa Umarnin babban Kwamandan Dr. Ibn Sina.


 A matakin farko, Mallaman sunyi masa nasiha da nusantar dashi hadarin wasa da addini tare da Shawartarsa da yakoma makaranta Dan gyara addininsa, inda nan take *Al'amin G fresh* Kano material yayi alkawarin gyara al'amuransa kuma yasaka hannu a takarda idan yasake Hukumar Hisbah zata dauki mataki  na gaba akansa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post