Saurayi Ya Angwance Da Amaryarsa Bayan ganin Hotunanta Da Kawarta Ta Wallafa Akan Status Din WhatsApp


Wani biki da aka yi ya ja hankalin al'umma musamman masu yin amfani da kafafen sada zumunta na zamani wanda wani mutum ya auri matarsa bayan yaga hotunanta da kawarta ta wallafa status dinta na whatsapp. 


Tun a ranar 14 ga watan Janairu 2021 kawarta ta saka hotunan budurwar a kan whatsapp status dinta. Inda na nemi ta turo min lambarta, har muka fara magana da ita. Yanzu anyi aure sati daya Alhamdulillah, cewar angon. 


Tun bayan wallafa hotunan bikinsu jama'a da dama sukai ta bayyana ra'ayoyinsu inda wasu ke yabawa kawar amaryar da ta bayar da number wayar ta ganin ba kasafai hakan ke faruwa ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post