Jaruma Saratu Daso Ta Nemi Tallafi Domin Yin Shagalin Zagayowar Ranar Haihuwarta - Android Pols


Fitacciyar jarumar Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo wacce aka fi Kira da Daso, ta fito da wani sabon salo na yin bikin murnar zagayowar ranar haihuwa inda ta nemi masoyan ta da su tura mata kuɗi don taya ta murna.


A wani saƙo da ta wallafa a soshiyal midiya ranar Laraba, Daso ta yi wannan sanarwar tare da yin murnar ranar da ta ƙara a cikin shekarun ta, inda ta ƙara da cewa: 


“Amma ni ba na yin taron mutane wai dan murnar cikar shekara, amma ga bank details ɗi na nan ana iya tura min kuɗi don taya ni murna. Don haka ga Lambar asusun ajiya ta na banki nan ga duk wanda zai tura mini”.


Jama’a dai da dama sun yi mata fatan alheri tare da roƙon Allah ya ƙara shekaru masu albarka.


Jarumar ‘yar wasan barkwanci ta wallafa lambar asusun ajiyar nata ba tare da ɓata lokaci ba.


Kawo yanzu dai babu wani bayani akan adadin kudin da masoyanta suka turama ta. Shin a ganin ku abinda ta yi ya dace? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post