HOTUNA: Dattijo mai shekaru 88 ya shiga makarantar Firamari ta yara a jihar Kano


Wani labari da ya jawo cece-Kuce kan Yadda wani dattijon mutum mai shekara kusan 90 ya shiga makarantar Firamari don yin Ilimi. 


Dattijon mai suna Abubakar Muhammad Barinjimi ya shiga ajin makarantar Firamare ta Model ta hadin Gwiwar Najeriya da Masar dake jihar Kano (Nigeria-Egyptian Model School).


Wannan dai za'a iya cewa bakon lamari ne da ba'a saba ganin irinshi ba, duk da ana samun wasu dattijai masu shekaru da suke shiga makaranta sai dai suna shiga ne irin daidai da masu shekarunsu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post