Budurwa ta kai ƙarar saurayinta Kotu kan yaɗa tsiraicinta a Facebook


Wata budurwa a Kano ta maka saurayinta a kotun Shari’ar Musulunci kan barazanar yada hoton tsiraicinta a Facebook.


’Yan sanda sun gurfanar da matashin a gaban kotun mai shari’a Nura Yusuf Ahmad, da ke unguwar Gama PRP a Karamar Hukumar Nassarawa, bisa tuhumar tsoratarwa.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, mai gabatar da karar, Aliyul ‘Abidin, ya shaida wa kotun cewa budurwar ta janye sakamakon wanda ta shigar da karar a kansa saurayinta ne.


An zargi matashin da yunkurin bata wa budurwa suna, bayan ya yi mata barazanar yada hoton tsiraicinta a Facebook, wanda hakan na iya bata mata suna.


Tun da farko saurayin ya yi wa budurwar barazana ne domin ta saya masa waya.


Sai dai bayan janye kararta, kotun ta sallami matashin da ake tuhuma, inda ta gargade shi kan yi wa mutum barazana.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post