An yi jana’izar wasu ’yan uwa da masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan 60 daga hannun iyalansu.
Lamarin dai ya faru ne a garin Dogo na yankin karamar Hukumar Lau a jihar Taraba. Kamar yadda shafin Punch ya rawaito.
Tun da farko dai masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da wasu ’yan gida daya su uku a unguwar Garin Dogo, inda suka bukaci mahaifinsu, Alhaji Musa Falke, dillalin shanu ya biya su Naira miliyan 100, amma sai suka biya N60m bayan tattaunawa.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudaden a cikin tsabar kudi kuma a kawo musu kudin a kan babur.
Maharan sun kashe direban motar, wani dan makiyayin shanun, wanda ya je ya kai kudin fansa a wani dajin da ke kusa da kauyen, wadanda suka yi garkuwa da su sun kashe shi bayan sun kashe 'yan uwansa.
Kawo yanzu dai an yi jana'izarsu kamar yadda addinin musulunci ya tanadar. Muna fatan Allah ya baiwa iyalinsu hakurin wannan babban rashin da suka yi amin.