Wata mata ta yi kokarin tilasta wa jami’an jirgin Southwest Airlines da ya tashi daga Houston zuwa Columbus, da Ohio yin saukar gaggawa a Little Rock, Arkansas a ranar Asabar din da ta gabata, bayan da ta yi ikirarin cewa Yesu ne ya bata umarnin ta bude kofar jirgin.
Bayanan da kotun Arkansas sun ce matar mai shekaru 34 ta nufi kujerar baya a cikin jirgin, inda ta rika kallon kofar da ake amfani da ita wajen fitar gaggawa.
A cewar kotun, guda daga cikin jami’an jirgin ya shaidawa matar ko dai ta shiga bandaki idan amfani za ta yi da shi, ko kuma ta zauna.
Haka zalika, daya daga cikin ma’aikatan jirgin ya shaidawa kotun cewa, matar ta tambaye su cewa tana so a bude mata taga, amma lokacin da ta samu amsar da bata yi mata ba sai ta yi amfani da karfinta wajen kokarin bude kofar jirgin.
Bayanai sun ce lokacin da ake ta kai ruwa rana da matar, jirgin ya yi nisan taku 37,000 tsakanin sa da kasa.
Wani fasinja ya bayyana cewa "lokacin da matar ke kokarin bude kofa," ya yi kokarin ya taimaka a tsare ta, inda suka rika kokawa a kasa, inda daga bisani ne ta cije shi a cinyar sa.
Rahotanni sun nuna cewa a lokacin ne matar ta fara dukan kanta a jikin jirgin sannan daga baya ta ce, "Yesu ya gaya mata ta tashi zuwa Ohio kuma Yesu ya ce mata ta bude kofar jirgin."