Wata mata ta hada baki da masoyinta sun binne jaririn da suka haifa da rai a cikin masai


Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wata mata ‘yar shekara 30 mai suna Balaraba Shehu bisa zargin binne jaririn da ta haifa da rai a cikin bandaki.


Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 3 ga Disamba, 2022. 


Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 02 ga watan Disamba da misalin karfe 23:50 a kauyen Tsurma da ke karamar hukumar Kiyawa ta jihar. 


Shiisu ya ce bayan da ‘yan sanda suka samu rahoton, an tattaro tawagar ‘yan sanda inda aka zarce zuwa wurin da lamarin ya faru.


“Bayan samun rahoton, wata tawagar ‘yan sanda ta taru suka wuce inda aka aikata laifin. Da isar su jami’an tsaro sun tono jaririn da aka haifa daga cikin masai inda mahaifiyar da ake zargin ta binne shi. An kama wadannda ake zargin kuma yanzu haka suna hannun ‘yan sanda,” inji shi. 


Ya kara da cewa an garzaya da jaririn zuwa babban asibitin Dutse, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa. 


Hukumar ta PPRO ta ce binciken farko ya kai ga kama wani Amadu Sale mai suna Dan kwairo mai shekaru 25 a kauyen Akar da ke karamar hukumar Kiyawa.


A cewarsa, ana zargin Amadu da laifin yiwa Balaraba ciki wanda ta haifi jaririn har suka hada baki da Balaraba don binne jaririn bayan ta haihu.


Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP Emmanuel Ekot Effiom, ya bayar da umarnin a mika karar zuwa SCID Dutse, domin gudanar da sahihin bincike.


Rahoton ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike akan su. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post