Tirkashi: Yadda Aka sha Shagalin bikin haihuwar wani dan akuya a Kano


Wata mata ta yi bikin haihuwar wani dan akuya da aka haifa mata a ranar Laraba a unguwar Maikalwa dake kan titin zuwa Zaria a jihar Kano.


Tarin mutane ne suka halarci wajen sunan har da mahaifiyar jaririn dan akuyar da aka haifa wanda aka radawa suna Nadira.


Kuma any girki sosai na abinci inda aka ci aka sha har da chashewa, inda DJ ya dinga kida da waka mata ana cashewa duk don nuna farin cikin samun dan akuyar.A kuma zantawar mu, da mamallakiyar wannan Akuya da ta santalo jariri, ta bayyana mana cewar, ta shirya bikin ne domin bayyana farin cikinta, kan sake haihuwar wannan Akuya, bayan da ta shafe tsawon shekaru batare da ko ɓatan wata ba.


kuma an gudanar da sunan a rana ta goma ne, a madadin kwanaki 7 da aka saba, sakamakon gaza halartar mai samar da sauti wurin bikin, tun a ranar Lahadi, wacce ta kasance rana ta bakwai da haihuwar jaririn.


Shi ma Mr. DJ, da ya yi Aikin samar da sauti a wurin, ya bayyana mana daɗin da ya ji, sakamakon cika Aljihunsa da ya yi, da kuɗaɗen da aka dinga lika masa.


Su kuwa, wasu daga cikin mahalarta, bayyana lamarin su kai a matsayin ''daɗin duniya'', duba da yadda ya kasance sabon al'amari da ba a saba gani ba, a wannan yanki na mu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post