Tanzaniya ta soke bikin ranar samun 'yancin kai, don yin amfani da kasafin kudin Wajen gina dakunan dalibai


Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta soke bikin ranar samun 'yancin kai da aka shirya gudanarwa a ranar Juma'a, 9 ga watan Disamba.


Samia Hassan ta ba da umarnin a yi amfani da kasafin kudin bikin ranar ‘yancin kai karo na 61 wanda ya kai dalar Amurka 445,000 domin gina dakunan kwanan yara masu bukata ta musamman. 


Za a yi amfani da kudin ne wajen gina dakunan kwanan dalibai takwas a makarantun firamare a fadin kasar.


Karamin Ministan Tanzaniya, George Simbachawene, a ranar Litinin ya ce an fitar da kudaden. Ya ce kasar da ke gabashin Afirka za ta yi bikin ranar samun 'yancin kai ta hanyar tattaunawa da jama'a kan ci gaba.


Gwamnatocin Tanzaniya da suka gabata sun sha soke bikin. A shekarar 2015 ne shugaban kasar na wancan lokaci John Magufuli ya soke bikin tare da karkatar da kudaden wajen gina hanya a babban birnin kasuwanci na Dar es Salaam.


A shekarar 2020 ma ya yi haka kuma ya ba da umarnin a yi amfani da kasafin kudin wajen siyan kayayyakin jinya.


Dubban mutane ne daga kasar Tanzania da makota suke ta yabawa shugabar kasar kan wannan mataki da ta dauka na inganta rayuwar yara dalibai. 


Har a Najeriya ma dai jama'a suna ta bayyana ra'ayoyinsu inda wasu ke fatan ace Najeriya tana yin irin hakan day an samu cigaba. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post