Mahauci ya dabawa mahaifinsa wuka lokacin da yake yin sallah a garin Zaria


Kotun Majistare dake zamanta a birnin Zariya dake jihar Kaduna ta tsare wani matashi kan zargin dabawa mahaifinsa wuka a lokacin da yake Sallah a masallaci. 


Shafin Aminiya ya rawaito cewa matashin da ake zargi dan shekaru 21 ana tuhumar sa da yunkurin kashe mahaifin sa a lokacin da yake yin sallah a wani masallaci dake unguwar Rimin Tsiwa a birnin Zariya. 


A Zaman Kotun an nemi alkali Ramatu Dalhatu ta bayar da belin matashin sai dai ta ki amincewa ta bayar da belinsa inda tace a saka shi a kurkuku har zuwa lokacin da ma'aikatar shari'a ta Jihar Kaduna ta yanke shawara akan lamarin. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

  1. ALLAH YA KARE MU DAGA SHARRIN WAN NAN ZAMANI.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post