HOTUNA: Jarumar Shirin Kwana Casa’in Ikilima Yusuf Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarta
Ikilima Yusuf jaruma dake fitowa a cikin shirin kwana casain mai dogon zango ta yi bikin cikar ta shekaru 26 a duniya. 


Jarumar ta yi bikin walimar ranar zagayowar haihuwarta a ranar Asabar wanda kawayenta da yan Kannywood suka halarci taron. 


Shafin Film Magazine ya rawaito cewa anyi walimar ne a Kano kuma maata yan Kannywood da suka halarci walimar akwai Safiya Adam, Rashida Adamu Abdullahi da sauransu. 


Bayan kammala cin abinci anyi kide-kide da raye-raye tare da cahsewa. Bayan hakan jarumar ta yi jawabin godiya musamman ga wadanda suka halarci walimar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post